Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

  • Wasu yan kasuwa guda biyu yan asalin jihar Abia sun shirya lale makudan kuɗi Miliyan N200m don siya wa mutum biyu Fom a APC
  • A wata sanarwa da suka fitar a Abuja, fitattun Attajiran sun ce sun gano kwarewa da salon mulki a jikin Sanata Ahmad Lawan da Orji Kalu
  • Sun bayyana cewa matauƙar kusoshin siyasar biyu sun shirya, to zasu saya musu Fom a karshen makon nan

Abia - Wasu Fitattun ƴan ƙasuwa daga jihar Abiya sun shirya fitar da Cakin makudan kudi Miliyan N200m ga ƙusoshin APC biyu don saya musu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa.

Punch ta tattaro cewa yan kasuwan, Ukaegbu James da Nnanna Kalu, sun shirya wannan abun bajinta ne ga shugaban Sanatoci, Ahmad Lawan, da kuma Sanata Orji Kalu.

Jami'iyyar Alla Progressive Congress.
Fitaccen ɗan kasuwa ya lale miliyan N200m zai siya wa yan takarar shugabn ƙasa biyu Fom Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mutanen biyu haifaffun Igbere, ƙaramar hukumar Bende ta jihar Abiya sun bayyana shirin su ne a wata sanarwa da suka fitar a Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Farfesan wata Jami'ar Najeriya ya mutu awanni bayan kubuta daga hannun yan bindiga

Sun bayyana cewa ƙusoshin biyu, Lawan da kuma Kalu duk sun cancanci su gaji kujerar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a zaɓen 2023 dake tafe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar yan kasuwan kuma Attajirai, jam'iyyar APC na bukatar kwararre kuma jagoran mai sadaukarwa wanda ya san Najeriya.

A sanarwan suka ce:

"Idan har dagaske muke, muna bukatar shugabanni da zasu kawo mana sakamako mai kyau kamar Lawan da Kalu."
"Lokaci ya yi da zamu gabatar da zaɓi nagari saboda ba bu sauran kofar rubuta sakamakom bogi kuma a shirye muke mu lale miliyan N200m zuwa ƙarshen makon nan domin siya musu Fom."
"Mun gamsu da kwarewar su a tarihi, kwarewa a shugabanci, jagoranci da sauran nagartar da mutanen biyu ke da shi."

Ina da yaƙinin wanda zai gaji Buhari- Sanata Gaya

A wani labarin kuma Sanata Kabiru Gaya na Kano ya bayyana sunan ɗan takarar da yake ganin zai lashe zaben ta ɗare mulkin Najeriya a 2023

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Sanata Kabiru Gaya mai wakiltar Kano ta kudu ya ce ba shi da tantama kan wanda zai gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a 2023.

Sanata Gaya ya bayyana cewa duba da kwarewar mataimakin shugaban ƙasa da sanin halin da ake ciki, shine zai ɗare mulkin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel