Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

  • Hadarin mota ya ritsa da sama da mutum hamsin masu ziyarar Masallacin Madinatul munawwarah
  • Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum takwas sun rasa rayukansu a wannan mumunan harin mota
  • Miliyoyin Musulmai daga fadin duniya suna zuwa kasar Saudiyya cikin watar azumi don gabatar da ibadar Umra

Labari da duminsa daga kungiyar Red Crescent a kasar Saudiyya na nuna cewa mota dauke da maniyyata masu ziyarar Masallacin Annabi (SAW) dake Madina sun samu hadari.

Haramain Sharifain ya ruwaito cewa motar mai dauke da mutum 51 ta yi juyi kan babban titi kuma mutane da dama sun jikkata.

Kawo yanzu da muke kawo rahoto an yi rashin rayuka takwas.

Jawabin yace:

"Wata motar Bas dauke da masu ziyara da maniyyata 51 ta kife a titin Hijra a Madinah Al Munawarrah yau kuma mutane da dama sun jikkata, 8 sun mutu."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Madina
Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama Hoto: Haramain Sharifain
Asali: UGC

Gwamnatin Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeran Hajji 43,000 bana

A wani labarin kuwa, Gwamnatin kasar Saudiyya ta baiwa Najeriya kujerun Hajji 43,000 a shirin ibadar Hajjin da za'a yi bana 2022.

Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi daga cikin hukumar alhazai ta kasa NAHCON sun ce nan ba da dadewa ba hukumar zata sanarwa yan Najeriya.

Legit ta tuntubi daya daga cikin kwamishanonin hukumar NAHCON wanda ya tabbatar da cewa lallai an baiwa Najeriya kujeru sama da 40,000 bana amma ya bukaci mu sakaye sunansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel