Buhari Ba Zai Amfana Da Komai Ba Idan Dariye Da Nyame Suka Mutu a Gidan Yari, Femi Adesina

Buhari Ba Zai Amfana Da Komai Ba Idan Dariye Da Nyame Suka Mutu a Gidan Yari, Femi Adesina

  • Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce Buhari ba zai karu da komai ba don tsohon gwamnan Filato da na Jihar Taraba, Joshua Dariye da Jolly Nyame sun mutu a gidan yari
  • Adesina ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a yayin da aka yi hira da shi a tashar talabijin din Channels inda ya ce kwamitin tarayya ta jiha ce ta amince da yafewa tsoffin gwamnonin da wasu mutane 157
  • Kakakin shugaban kasar ya ce an yafewa Nyame da Dariye ne saboda ganin halin rashin lafiya da kuma shekarunsu da suka yi nisa, hakan ya sa aka duba mummunan yanayin da suke ciki aka yafe musu

Femi Adesina, Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu karuwar da Buhari ze yi don tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye da tsohon gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame sun mutu tsare a gidan gyaran hali, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

A ranar Juma’a Adesina ya bayyana hakan yayin da aka tattauna da shi a gidan Talabijin din Channels a wani shirinsu na ‘Siyasa a yau’ wanda The Punch ta kula da shi.

Buhari Ba Zai Amfana Da Komai Ba Idan Dariye Da Nyame Suka Mutu a Gidan Yari, Femi Adesina
Babu abinda Buhari zai karu da shi don Dariye da Nyame sun mutu a gidan yari, Femi Adesina. Hoto: Joshua Dariye.
Asali: Twitter

A cewarsa, Kwamitin tarayya ta jiha ce ta amince da yafe wa tsofaffin gwamnonin tare da sauran ‘yan gidan yari 157 bayan Kwamitin bai wa shugaban Kasa shawarwari akan Yafiya ta ga cancantar hakan.

Ya bayyana dalilin yafe musu

Kakakin ya ce an yafewa Dariye da Nyame ne bayan ganin shekarunsu sun yi nisa tare da matsalolin lafiya da suke fuskanta, rahoton The World News.

An daure tsofaffin gwamnonin ne bayan kama su da laifin satar N2.7bn, kuma mambobin jam’iyyar APC ne.

Akwai kungiyoyi masu zaman kansu da dama da suka dinga caccakar shugaban kasa inda suka ce yafe wa Dariye da Nyame zai bai wa masu rashawa kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Nyame Da Dariye: Ka Janye Afuwar Ko Mu Kaɗa Maka Ƙuri'ar Rashin Gamsuwa, Ƙungiyoyin Arewa 19 Sun Gargaɗi Buhari

Amma a ranar Juma’a da Adesina ya yi bayanin, ya ce;

“Ban ga ta inda yafiyar ta kawo cikas da yaki da rashawa ba.”

Adesina ya ce babu abinda gwamnati za ta karu da shi don sun mutu a gidan yari

Ya kara da cewa:

“Kwamitin yafiyar wacce ta zauna ta yi dubi da shawarwarin da aka ba ta ce ta tantance wadanda suka nemi a yafe musu.
“Dalilin da ya sa aka amince da yafe wa tsoffin gwamnonin shi ne shekaru da kuma rashin lafiya. Da me mutun zai karu don sun mutu a gidan yari? An samu labarin cewa suna cikin mawuyancin yanayi.
“Sababin yafe musu shi ne shekaru da kuma rashin lafiya; babu abinda gwamnati za ta karu da shi don tsofaffin gwamnonin sun mutu.”

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164