Alheri danko: Daga kyautar N100, mabaraci ya samu sakayyar N100k nan take

Alheri danko: Daga kyautar N100, mabaraci ya samu sakayyar N100k nan take

  • Wani dan Najeriya ya yiwa wani mabaraci da ke kan keken guragu abin kirki bayan da ya ba shi N100 ya ci abinci
  • Dan Najeriyan ya roki mabaracin ne kan ya ba shi kudi ya samu abin da zai ci, lamarin da ya narkar da zuciyarsa
  • Mabaracin nan haka ya kukuta ya yi wa mutumin kyautar N100, wannan yasa dan Najeriyan ya ba shi kyautar N100k

Wani dan Najeriya mai suna De General ya sanya farin ciki a fuskar mabaraci inda ya ba shi tsabar kudi N100k a nan take.

De General ya yi shiga kamar mabukaci, inda ya yi niyyar sakawa duk wani mabaracin da ya ba shi taimakon kudi, shi kuma Ibrahimu daga jihar Zamfara ya yi sa'ar cin jarrabawar.

Wani faifan bidiyo mai kayatarwa da @iam_degeneral ya yada Tiktok da aka dauka lokacin da ya roki mabarancin da ke kan keken guragu ya bashi kudi zai ci abinci ya nuna yadda lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

Yadda kyautar N100 ta ja mas alherin N200k
Alheri danko: Daga kyautar N100, mabaraci ya samu sakayyar N100k nan take | Hoto: @iam_degeneral
Asali: UGC

Da farko Ibrahimu ya bayyana kamar a firgice amma sai ya daure ya ba De General N50.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da De General ya yi godiya, mabaracin ya ninka kudin ta hanyar fitar da wata gudan N50.

Alherinsa ya kai shi ga samun rabo

Hakan ya motsa De General wanda nan da nan ya bayyana ma mabaracin cewa shi ba mabukaci ba ne kawai dai ya yi shigan burtu ne.

Ya nuna ma mabaracin inda motarsa take, ya kuma yabawa Ibrahimu bisa kyautata masa da ya yi.

Nan take ya baiwa Ibrahimu kyautar N100k, abin da ya bawa mabaracin matukar mamaki.

Kalli bidiyon:

Yan Najeriya sun sha mamaki

moridiatoyindamola ya ce:

"Ya matukar motsa ni a cikin zuciya, mutumin kirki ne ❤️ mun gode da taimakonsa Allah madaukakin sarki ya cigaba da rage maka radadin rayuwa babban mutum."

Kara karanta wannan

Ta yi daidai: Martanin jama'a yayin da magidanci ya dauko karuwa, ta saci kwal din N6m a gidan abokinsa

donblinkmillion ya ce:

“Allah ya albarkace ka bisa nuna soyayya ga mutane, ba sai ka yi arziki ba kafin ka taimaki wasu.
"Duk da yana cikin yanayi, amma zai iya taimakawa wasu."

Chikezie Onyinyechi

"Ya kamata su taimaka masa ya isa gidansa fah, wurin nan bai da aminci sosai, duba wanda ke bayansa ya yi kama da Anin."

Collins ya ce:

"The General! "Hmmmm, Allah zai cigaba da saka maka albarka ya kuma daukaka ka bisa irin halin kirki, wannan faifan bidiyon ya sa ni kuka, Allah ya maka albarka."

Kyakkyawan karshe: Yadda mutuwa ta dauki matashin Limami a tsakiyar Sujadar Tahajjud

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta samu labarin rasuwar wani Alaranma mai suna Sani Lawal wanda ya rasu a lokacin da yake ibadar sallar dare a watan Ramadan.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga majiyoyi da dama, Sani Lawal ya rasu ne a daidai lokacin sujada, yana limancin sallar tahajjud a ranar Asabar dinnan.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Buhari Ya Yi Magana Kan Gaskiyar Bacewar Naira Tiriliyan 89 a Bankuna

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin dazu da safe da kimanin karfe 8:00 na safe a unguwarsu da ke Layin MB, Samaru, karamar hukumar Sabon Gari, Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel