2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

  • Shirye-shirye kan zaben shugaban kasa na 2023 ya kai matsayi mai dumi yayin da ake ta sanya ido kan wa zai gaji shugaba Muhammadu Buhari
  • Fiye da 'yan takara 30 aka samu a fadin jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP, a halin yanzu
  • Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna ya yi hasashen yadda 'yan takarar shugaban kasa za su fito daga PDP da APC

Najeriya - Gabanin babban zaben shugaban kasa na 2023, masana harkokin siyasa da masu ruwa da tsaki sun fara hasashen wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanata daga Kaduna, kuma mai rajin kare hakkin bil’adama, Shehu Sani ya bayyana hasashensa kan yadda zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyun siyasar Najeriya APC da PDP za su kasance.

Kara karanta wannan

Buhari ga shugabannin APC: Ku haramtawa PDP mulki a 2023 kamar yadda kuka yi a 2015

Yadda za a zabi 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyun PDP da APC
2023: Shehu Sani ya bayyana yadda ‘yan takarar shugaban kasa na APC da PDP za su fito
Asali: UGC

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Twitter, @ShehuSani, ya bayyana cewa za a tantance dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki ne bisa ga wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa za a yanke shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ne bisa la’akari da tattaunawar jajibirin zaben fidda gwanin da za a yi kan zaben fidda gwani na PDP.

Ya rubuta a Twitter cewa:

“An fadi komai, an yi komai; dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ba kowa bane face wanda shugaban kasa yake so, kuma za a kira shi da ijma'in (jam'iyya).
"Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa zai fito ne daga sakamakon yarjejeniyar da aka kulla a jajibiri, ko kuma sakamakon zaben fidda gwani mai zafi."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

A wani labarin, yayin da Najeriya ke kara kusanto da babban zaben 2023, a ranar Juma'a masu zanga-zangar sun mamaye ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja, suna kira gare shi da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Jama'ar sun kunshi maza da mata da matasa, inda suka mamaye ofishin dauke da alluna da takardu na neman tsohon shugaban kasar ya shiga takarar shugaban kasa, Vanguard ta ruwaito.

Wasu daga cikin fastocin da ke dauke da hotunan Jonathan an rubuta: "GoodLuck Jonathan, dole ne ka tsaya takara"

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.