2022: Jerin adadin kujerun Hajji da kowace jiha ta samu a Najeriya, wasu jihohi hudu ba su da ko ɗaya
- Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce jihohi hudu a Najeriya ba zasu samu gurbin sauke farali ko ɗaya ba a 2022
- Hakanan shugaban NAHCON, Zikurullah Hassan, ya ce yanayin tashin abubuwa a duniya ne ya jawo ƙarin kudin Hajji
- Ya kuma bayyana yadda suka raba wa jihohin Najeriya da Abuja kujerun da Saudiyya ta ware wa kasar nan
Abuja - Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta ce jihohin Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom da Imo ba su samu kujera ko ɗaya ba a wannan shekarar.
Daily Trust ta ruwaito cewa kuɗin aikin Hajji na bana 2022 ka iya ƙaruwa da sama da kashi 50, a cewar hukumar NAHCON.
A shekarar 2019, Mahajjata sun biya miliyan N1.5m, bisa haka duk mutanen da suka aje kuɗin su tun shekarar 2020, za su ƙara akalla Miliyan ɗaya a sama.
Ina da kwarin guiwa da izinin Allah wannan ɗan takarar ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan Kano ya magantu
Shugaban NAHCON, Zikirullah Hassan, ya ce waɗan nan jihohi hudu ba zasu samu gurbi ko ɗaya ba saboda ba su da lasisi daga hukumar.
Sai ɗai ya ƙara da bayanin cewa idan wani Musulmi daga waɗan nan jihohin na da niyyar sauke farali, hukumar NAHCON zata taimaka masa ya cika burinsa.
Hassan ya yi wannan jawabi ne ranar Alhamis a Abuja, a wurin taronsa da rassan NAHCON na jihohi a wani ɓangare na fara shirye-shiryen tunkarar Hajjin bana 2022.
Meyasa kuɗin Hajji ya tashi?
Ya ce an samu karin kuɗin Hajji da aƙalla kashi 50% saboda halin tattalin arzikin da ake ciki a duniya da sauran wasu dalilai.
A kalamansa ya ce:
"Karin kuɗin kujera da muka tsinkaya da kashi 50 ya faru ne saboda a 2019 farashin Dala na N306, amma yanzun ya kai N410 kan kowace Dala ɗaya. Mun san cewa kashi 97 na harkokin aikin Hajji kama daga Abinci da kuɗin jirage sun doagara ne da Canjin kudi."
"Ƙasar Saudiyya ta ƙara harajin VAT daga kashi 5 zuwa kashi 15% sun kuma gaya mana sun ƙara zuba hannun jari a Minna da Arfa."
Ya ƙara da cewa kowane mahajjaci ya tabbata ya kammala allurar rigakafin COVID19 har zuwa ta uku, kuma wajibi ne yin gwajin PCR.
Haka nan game da yadda zasu yi da Mahajjatan da suka biya kudi tun baya, shugaban NAHCON ya ce zasu zabi Mahajjatan bana ta hanyar wanda ya fara zuwa tare da amafani da jadawalin kaso 40 ga sabbi, kaso 60 ga na baya.
Yadda aka raba kujeru zuwa sauran jihohin Najeriya
Hassan ya ce game da gurbi 43,008 da Saudiyya ta ba Najeriya, kujeru 33,976 zasu tafi zuwa jihohi, 9,032 ga masu tafiyar kai da kai, da kuma 3,398 na masu ruwa da tsaki
Daga cikin kujeru 33,976 da aka kasaftawa jihohi, Kaduna ta samu 2,249; Sokoto-2,404; Neja- 2,256; Kano-2,229; Katsina-2,146; Kebbi-2,128; Legas-1,562; Bauchi-1,363; Adamawa- 1,166; Abia-6; Anambra-17; Benuwai- 103; Borno-1,195; Kuros Riba- 29; Delta-19.
Sauran kuma sun samu Ebonyi, 51; Edo, 94; Ekiti, 86; Enugu, 13; FCT, 1,538; Gombe, 1,005; Jigawa, 614; Kogi, 319; Kwara, 1,406; Nasarawa, 684; Ogun, 497; Ondo, 191; Osun, 460; Oyo, 629; Filato, 824; Taraba, 651; Yobe, 860; Zamfara 1,303 da kuma hukumomin tsaro, 239.
A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya umarci hafsoshin tsaro su ceto dukkan mutanen da yan ta'adda suka sace a faɗin Najeriya
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwarsa kan karuwar matsalar tsaro a faɗin kasa yayin taronsa da Hafsoshin tsaro.
Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin da suka shafi tsaro (NSA), Babagana Monguno, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai na gidan gwamnati jim kaɗan bayan kammala taron.
Asali: Legit.ng