Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Tura Jami'anta Zuwa Duk Masallatai

Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Tura Jami'anta Zuwa Duk Masallatai

  • Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tura jami’anta masallatan da ke kananun hukumomi 44 a cikin jihar don tabbatar da an yi Tahajjud cikin tsanaki
  • Dama an fara Tahajjud ne a ranar Alhamis da dare, kuma hukumar ta yi hakan ne don samar da kariya ga masu ibadar daga bata-gari
  • Kwamanda Janar na rundunar, Dr Harun Ibn-Sina ne ya saki wata takarda wacce ta sanar da hakan a ranar Alhamis a Kano

Kano - A ranar Alhamis, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tura jami’anta zuwa masallatan da ke gabadaya kananun hukumomi 44 da ke jihar don tabbatar da an yi Tahajjud na watan Ramadan cikin tsanaki, wanda aka fara a ranar Alhamis da dare.

Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Tura Jami'anta Zuwa Duk Masallatai
Jami'an Yan Hisbah Na Kano a cikin motarsu. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce Kwamanda Janar na rundunar, Dr Harun Ibn-Sina ya saki a ranar Alhamis a Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Ana yin Tahajjud’, wanda tsayuwar dare ne da musulmai na kwarai su ke yi don neman yardar Ubangiji a cikin kwanaki 10 na karshen watan Ramadan kamar yadda Ibn-Sina ya ce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ibn-Sina ya ja kunnen bata-gari daga kai wa masu Tahajjud farmaki

Ya ja kunnen bata-gari akan kai wa masu ibadar famaki yayin da ake tsaka da Tahajjud din ko kuma kirkirar ayyukan ta’addanci.

A cewar Ibn-Sina, kamar yadda NAN ta nuna, duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

A wani rahoton daban, Hukumar Hisbah reshen jihar ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: