Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba

Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba

  • Rahoton da muke samu daga majiyoyi ya bayyana cewa, an gano mafakar 'yan ta'addda a jihar Taraba, an ragargaje su
  • An ce an hallaka wasu yayin da sojin kasa suka kama wasu da dama daga cikin 'yan bindigan da suka addabi yankin
  • Rundunar 'yan sandan jihar Taraba sun tabbatar da faruwar lamarin, sun yi karin haske akan farmakin

Taraba - Rundunar sojin saman Najeriya ta lalata maboyar gungun ‘yan bindiga da dama a kewayen kauyen Kambari da ke karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

Jiragen saman NAF sun yi ruwan bama-bamai a yankunan inda suka kashe ‘yan bindiga da dama a wani samame da suka fara kwanaki uku da suka gabata.

A farmakin akwai dakarun kasa da suka kama ‘yan bindiga da dama da 'yan leken asirinsu a kewayen Gassol da Karim Lamido duk dai a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Harbi Mutane, Sun Sace Dabobi Masu Yawa

Yadda sojin sama suka ragargaji 'yan bindiga
Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sai dai kuma an kashe wasu mutane uku da ba su ji ba ba su gani ba bisa kuskure a kusa da Kwatan Nanido da ke karamar hukumar Gassol.

Majiyar 21st Century Chronicle ta bayyana cewa, ‘yan bindigar da suka shafe watanni biyu suna cikin yankin Kambari, an ce su ne ke da alhakin mafi yawan sace-sacen mutane da kashe-kashe a kauyuka da dama da ke fadin kananan hukumomin Bali, Gassol da Karim Lamido

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce aiki ne na rundunar sojin sama kawai.

A cewarsa:

"Muna sane da aikin amma aikin sojojin saman Najeriya ne kawai kuma ba za mu iya cewa komai kan hakan ba."

Jerin Haɗurran Jiragen Sojojin Najeriya da Suka Faru a Cikin Shekarar 2021

Kara karanta wannan

Mu muka kai harin Bam mashaya a jihar Taraba, Kungiyar ISWAP

Wannan shekarar 2021 da ta gabata ta kasance mai cike da ƙalubale a Najeriya saboda samun haɗurran jiragen sama wanda ya laƙume rayuka da yawa.

Tun daga haɗarin farko a Abuja har zuwa wanda ya faru na ƙarshe a Zamfara, rundunar sojin Najeriya ta samu kaƙubalen hatsarin jiragenta hudu a 2021.

A ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairu, 2021, jirgin rundunar sojin sama (NAF) King Air 350 ya yi hatsari a kusa da Abuja, inda lamarin ya lakume rayukan baki ɗaya jami'ai Bakwai dake ciki.

A bayanan Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, jirgin ya yi haɗari ne jim kaɗan bayan tura saƙon cewa injinsa ya samu matsala.

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Harbi Mutane, Sun Sace Dabobi Masu Yawa

Yan bindiga sun sake kai hari a wani gari a Zamfara, inda suka raunata mutane da dama kuma suka sace dabobi da yawa da ba a tabbatar da adadinsu ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

TVC ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a kauyen Gabake da ke karamar hukumar Kauran Namoda a Jihar ta Zamfara.

Maharan sun afka kauyen da yammacin ranar Alhamis suka yi fafata da mutanen garin na fiye da awa biyu, kamar yadda TVC ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.