Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

  • A ranar Alhamis ne Mai girma Muhammadu Buhari ya yi buda baki tare da malamai da sarakuna
  • Shugaban kasar ya gayyaci malaman addini da sarakunan gargajiya domin shan ruwa a Aso Rock Villa
  • Muhammadu Buhari ya bayyana matsalolin da ake samu, tare da yin kira ga jagororin al’umman

Abuja - A ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu 2022, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karya azuminsa tare da malamai da sarakuna a Aso Rock Villa.

Jaridar Daily Trust ta ce Mai girma Muhammadu Buhari ya gayyaci malaman addini da sarakunan gargajiya ne domin su sha ruwa tare da shi a fadarsa.

A wajen buda-bakin, shugaban kasar ya shaida masu cewa babu gwamnatin da za ta iya shawo kan matsalar tsaro ba tare da hada-kai da malamai da sarakai ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

Buhari ya fada masu gwamnatinsa za ta cigaba da sauran muhimman shawarwarin da suke badawa domin ganin an kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya.

An rahoto Mai girma shugaban kasar yana cewa nauyi ya rataya a kan wuyan shugabanni a kowane mataki da su tashi-tsaye wajen tabbatar da an gyara kasa.

A karshe, ya ce nasarar jami’an tsaro ta rataya ne daga bayanan da suke samu a wajen al’umma a game da ‘yan bindiga, ya ce da yardar Allah, za a kawo karshensu.

Shugaban kasa a Aso Villa
Buhari tare da malamai da sarakuna Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Jawabin Muhammadu Buhari

“A yau matsalar rashin tsaro ta na cikin mafi girman kalubalen da Najeriya ta ke fuskanta a matsayin kasa.”
“Wannan gwamnati ta kashe dukiyar da ta fi ta kowace gwamnati domin ganin an kawo karshen rashin tsaro.”
“Mun saye kayan yaki na zamani domin inganta aikin sojoji da ‘yan sandan na yaki da tsageranci da ta’addanci.”

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

“Mun ware isassun kudi da ake bukata a cikin kundin kasafin kudin kasa domin abin da ya shafi harkar tsaro.”

Amma abin ya ci tura...

“Da zarar jami’an tsaro sun bukaci wani abu, ina yi maza in ba su. Amma matsalar ta mamaye Duniya.”
“Mafitar ita ce, kowa a cikin al’umma ya taka rawarsa wajen ganin an tunkari wadannan miyagun mutane.”

Malamai da Sarakuna sun yi magana

Sarkin kasar Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi yana cikin wadanda suka yi jawabi, har ya yabi kokarin gwamnatin nan wajen yakar annobar cutar COVID-19.

Rahoton ya ce sakataren kungiyar CAN, Barr. Joseph Daramola ya tofa albarkacinsa a taron.

Gara jiya da yau

A makon nan aka ji labari Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diriya ce sha’anin tsaro ya tabarbare yanzu a gwamnatin Muhammadu Buhari mai-ci.

Douye Diri ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen kawo zaman lafiya a Arewa, a lokacin da Buhari yake ganin an samu cigaba tun bayan 2015.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar Filato

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng