Bidiyon Yan Boko Haram 72 sun mika wuya ga Sojoji a Arewa maso gabas

Bidiyon Yan Boko Haram 72 sun mika wuya ga Sojoji a Arewa maso gabas

  • Sabbin Yan Boko Haram sama da saba'in sun mika wuya ga Sojoji a tafkin Chadi Arewa maso gabas
  • Sun ce sun gaji da halin yunwa da rikicin cikin daji kuma basu da wani zabi da ya wuce su ajiye makamansu su mika wuya
  • Sama da yan Boko Haram dubu ashirin sun mika wuya kawo yanzu ga Sojoji

Borno - Akalla sabbin yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 70 sun mika wuya ga jami'an Sojin Najeriya a karamar hukumar Dikwa, jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Leadership ta ce a rahoton da wani masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama, yace yan ta'addan sun mika wuya da kansu ne ga rundunar Operation Hadin Kai ranar Laraba.

Yace yan ta'addan sun ce sun gaji da halin yunwa da rikicin cikin daji kuma basu da wani zabi da ya wuce su ajiye makamansu su mika wuya.

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

A cewar majiyar:

"Wasu cikinsu sunce su manoma ne asalinsu amma yan ta'addan suka turkesu kuma yanzu suna farin cikin samun fita."

Wata majiya daga gidan Soja tace za'a bincikesu sosai kafin kaisu sansanin sauya tunani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Boko Haram
Sabbin yan Boko Haram 72 sun mika wuya ga Sojoji a Arewa maso gabas Hoto: Zagazola
Asali: Facebook

Ga bidiyonsu:

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Tiyata Kwamanda na rundunar “Operation Hadin Kai”, Christopher Musa, ya bayyana cewa adadin yan Boko Haram da suka mika wuya kawo yanzu ya kai 17,000.

Musa ya bayyana hakan ne ranar Juma'a lokacin da ya kai ziyara wajen shugabannin hukumar cigaban Arewa maso gabas, NEDC.

Ya bayyana cewa wannan adadi ya hada da mayaka, iyalansu da kuma wadanda aka tilasta shigar harkar Boko Haram.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha

Ya ce adadin masu mika wuyan na yawa kulli yaumin kuma hukumar na bukayar NEDC ta taimaka wajen kula da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel