2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya

2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya

Daga cikin biloniyoyi 2,668 na shekarar 2022 da Forbes ta fitar, mata kadan aka samu. An samu 327, kasa da 328 na shekarar da ta gabata (har da matan da dukiyarsu ta hada da ta mazansu, 'ya'ya ko 'yan uwa) suna da jimillar $1.56 tiriliyan fiye da ta shekarar da ta gabata da ta kai $1.53 tiriliyan.

Da yawa daga cikin hamshakan matan nan, 226 daga cikinsu sun samu dukiyarsu ne ta hanyar gado. Sun hada da mata uku na farko a duniya masu tarin arziki.

Akwai L'Oreal wacce ta gaji Francoise Bettencourt Meyers, Walmart, magajiyar Alice Walton da Julia Koch, wacce ta gaji masana'antun Koch bayan mutuwar mijinta David Koch a shekarar 2019.

2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya
2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya. Hoto daga forbes.com
Asali: UGC

A wannan shekarar, sabuwar biloniya da aka samu itama gado ta yi: Czechia Renata Kellnerova da 'ya'yanta hudu sun gaji dukiya da ta kai $16.6 biliyan bayan mijinta Peter Kellner ya rasu a mummunan hatsarin jirgin sama a watan Maris na 2021.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Jigo a Najeriya ya fusata kan kin hukunta wadanda suka kashe Deborah

Dari da daya daga cikin biloniyoyin mata na duniya duk masu nema ne da kansu, ma'ana su suka kafa kamfani ko kuma kamfanin hadin guiwa garesu, amma da kudinsu da suka nema ba wai gado ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar Forbes ta ruwaito cewa, daga ciki akwai Diane Hendricks, wacce suka kafa kamfanin Doris Fisher da kamfanin caca na Denise Coates.

Sabbin biloniyoyin wannan shekarar kuma fitattu sun hada da Rihanna, wacce mashahurin kamfanin kayan kwalliyanta yasa ta zama biloniya ta farko daga Barbados, Melanie Perkins, matashiya mai shekaru 34 wacce suka kafa Canva, da Melinda French Gates, wacce ta shiga jerin mata biloniyoyin duniya bayan samun dukiyarta a rabuwar aurenta da Bill Gates a tsakiyar shekarar 2021.

Amurka ta fi kowacce kasa yawan biloniyoyin mata a duniya inda take da 90, China na biye da ita mai 63 da suka hada da 11 daga Hong Kong, sai Jamus mai 35.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya Saka Gadaje a Ofisoshi Twitter, Ya Ja Kunne Kan Sharholiya Babu Aiki Tukuru

Ga jerin mata 10 na farko a cikin biloniyoyi mata 327 na shekarar 2022 da tarin dukiyar da suka mallaka:

1. Francoise Bettencourt Meyers

Ta mallaki dukiyar da ta kai $74.8 biliyan kuma ta samo ta ne daga kamfaninta mai suna L'Oreal. 'Yar asalin kasar Faransan ta kasance mace da ta fi kowa dukiya a duniya.

Ta fara bayyana a cikin biloniyoyin duniya ne a 2018 bayan mutuwar mahaifiyarta Liliane Bettencourt wacce ta taba kasancewa matar da tafi kowa kudi a duniya.

2. Alice Walton

Arzikin matar 'yar kasar Amurkan ya kai $65.3 biliyan.

Diyar ta Walmart, wanda ya kafa Sam Walmart, dukiyarta ta karu da $3.5 biliyan a shekarar da ta gabata. Ita ce matar da ta fi kowa arziki a duniya a 2020.

3. Julia Koch

Julia Koch mata ce da mijinta David Koch ya mutu ya bar mata dukiya da 'ya'yanta inda ta mallaka kashi 42 na masana'antun Koch, kamfani na biyu mafi girma mai zaman kansa a Amurka. Dukiyar 'yar asalin kasar Amurkan ta kai $60 biliyan.

Kara karanta wannan

Iyalai A Nigeria Na Hakura Da Ci Su Koshi Sabida Yanayin Tashin abinci

4. Mackenzie Scott

Tana da dukiyar da ta kai $43.6 biliyan tun bayan da ta rabu da Jeff Bezos, mamallakin Amazon a 2019.

Scott ta kasance shahararriyar mai taimakon jama'a a tarihi. Ta kyautar da $12.5 biliyan na dukiyarta ga kungiyoyi 1,250 a cikin kasa da shekara biyu.

5. Jacqueline Mars

Ta mallaki dukiyar da ta kai $31.7 biliyan. 'Yar kasar Amurkan ta gaji daya bisa uku na Mars Incorporated. Kakanta Frank C.Mars ya kafa kamfanin a shekarar 1911.

6. Gina Rinehart

'Yar asalin kasar Australia ta mallaki dukiyar da ta kai $30.2 biliyan. Ita ke shugabantar kamfanin hakar ma'adanai da noma na Hancock Prospecting Group wanda mahaifinta Lang Hancock ya kafa.

7. Miriam Adelson

'Yar Amurkan ta mallaki arzikin da ya kai $27.5 biliyan. Matar da mijinta Sheldon Adelson ya mutu, ta mallaka kusan kashi 50 na dukiyarsa a Las Vegas Sands a 2021.

8. Susanne Klatten

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

'Yar asalin kasar Jamus din ita ke da mallakin kashi 19 na kamfanin BMW wanda ta gada daga mahaifiyarta Johanna Quandt da mahaifinta Herbert Quandt, dan kasuwan da ya ceto kamfanin BMW daga rushewa a 1959. Klatan ta mallaki wani kamfanin kemikal a Altana.

9. Iris Fontbona

Dukiyar 'yar kasar Chile din ta kai $22.8 biliyan wacce ta same ta ta hanyar hakar ma'adanai.

Fontbona ita ce mai takabar fitaccen mai arzikin kasar Chile da ya mutu, Andronico Luksic, wanda cutar kansa ta kashe a 2005.

10. Abigail Johnson

Arzikinta ya kai $21.2 biliyan. 'Yar kasar Amurkan ce CEO ta Fidelity Investment tun 2014 bayan gadar mahaifinta Ned Johnson III da tayi wanda ya rasu a watan Maris.

Ita ke da mallakin kusan kashi 24.5 na dukiyar kamfanin.

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel