Innalillahi: Allah ya yi wa wani Sarkin Gargajiya a Osun rasuwa

Innalillahi: Allah ya yi wa wani Sarkin Gargajiya a Osun rasuwa

  • Duk wani mai rai zai ɗanɗana mutuwa, Allah ya karɓi rayuwar Sarkin kasar Ikoyi a jihar Osun, Yisau Bamitale Oyetunji Otunla, rasuwa
  • Basaraken ya samu kyakkyawar shaida daga bakunan mutanen da ya mulka, ya rasu yana da shekara 75 a duniya
  • Gwamnatin jihar Osun ta jajantawa iyalan gidan Masarauta da sauran mutane bisa wannan babban rashin na Uba

Osun - Basaraken gargajiya na ƙasar Ikoyi a jihar Osun, Oba Yisau Bamitale Oyetunji Otunla, ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Basaraken wanda aka naɗa wa rawanin Sarauta a shekarar 1987, ya shafe shekaru 35 a kan karagar Sarauta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sarkin ƙasar Ikoyi.
Innalillahi: Allah ya yi wa wani Sarkin Gargajiya a Osun rasuwa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mazauna ƙasar Ikoyi sun ba da kyakkyawar shaida a kan marigayi Sarkin, sun ce mulkinsa ya kasance na zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ku Ba Mu N200m Cikin Kuɗin Tallafin Man Fetur, Mu Koma Aji: ASUU Ta Roƙi Gwamnatin Buhari

Gwamnan Osun ya yi ta'aziyya

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, Funke Egbemode, ya fitar, gwamna Oyetola na jihar Osun ya yi wa gidan Sarauta ta'aziyya da kuma al'ummar ƙasar Ikoyi.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Gwamnatin Osun na jajantawa iyalan masarautar Olukoyi ta ƙasar Ikoyi, ƙaramar hukumar Isokan bisa rasuwar Sarki Yisau Bamitale Oyetunji Otunla, wanda ya koma ga Mahaliccinsa ranar Litinin yana da shekara 75."
"A shekaru 35 da ya shafe kan karagar sarauta, marigayi sarki ya kasance sanannen mutumin kirki mai sadaukarwa da kuma jawo mutanensa a jiki wajen nuna musu soyayya. Tabbas za'a yi kewan sa."
"Gwamnati da kuma mutanen jihar Osun suna masa Addu'a Allah ya yi masa rahama, haka nan kuma Allah ya ba iyalansa da mutanen ƙasar Ikoyi haƙuri na juriyar wannan babban rashi."

Kara karanta wannan

2023: Malamin Musulunci a Najeriya ya fito takarar shugaban ƙasa, ya nemi tallafin kuɗin Kanfe

A wani labarin na daban kuma Mataimakin Kwamishinan yan sanda ya yanke jiki ya mutu yana tsaka da aiki a Hedkwata

Mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar Bayelsa mai kula da sashin shugabanci ya rasu yana cikin aiki a Hedkwata.

Rahoto ya nuna cewa Mamacin ya yanke jiki ya faɗi a cikin Ofishinsa, aka yi kokarin kai shi Asibiti amma rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel