Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Yana Tsaka da Aiki a Ofis

Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Yana Tsaka da Aiki a Ofis

  • Mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar Bayelsa mai kula da sashin shugabanci ya rasu yana cikin aiki a Hedkwata
  • Rahoto ya nuna cewa Mamacin ya yanke jiki ya faɗi a cikin Ofishinsa, aka yi kokarin kai shi Asibiti amma rai ya yi halinsa
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya ce ranar ta zama ta baƙin ciki ga hukumarsu

Bayelsa - Mataimakin kwamishinan yan sanda mai kula da ɓangaren shugabanci, ACP Emmanuel Idowu Asufi, ya yanke jiki ya faɗi kuma Allah ya karɓi rayuwarsa yana cikin sauke nauyin dake kansa.

Daily Trust tace ACP Asufi ya yanke jiki ya faɗi ne a Hedkwatar yan sanda dake yankin Avom, Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa da yammacin Talata.

Kara karanta wannan

Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya yi luguden wuta kan kananan yara bisa kuskure a jihar Neja

Mutuwar ba zata da Babban ɗan sandan ya yi ta jefa hukumar yan sanda reshen jihar Bayelsa cikin kaɗuwa da damuwa.

Mataimakin kwamishina, ACP Emmanuel Idowu Asufi.
Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Yana Tsaka da Aiki a Ofis Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mamacin ɗan asalin ƙauyen Ekwanine na jihar Delta ne, kuma ya jima a kujerar mataimakin kwamishinan yan sanda na jiha mai kula da sashin shugabanci, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Ya jami'an yan sanda suka ji da rasuwar?

Mafi yawan jami'an yan sanda da suka yi aiki tare da mamacin sun kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwarsa farat ɗaya.

Wani ɗan sanda dake aiki da rundunar Operation Puff Adder a jihar Bayelsa ya shaida wa manema labarai cewa:

"Mun kaɗu sosai, da yawan mu sun ga shigowarsa Hedkwata yana murmushi, yana gaisawa da kowa. Amma mun kaɗu da labarin faɗuwarsa ta zo mana, sun yi gaggawar kai shi Asibiti, aka tabbatar ya cika."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: N100m zamu sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC

Kakakin yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da mutuwar ACP Asufi, ya ce ranar ta zama ta bakin ciki ga hukumar yan sanda.

A wani labarin na daban kuma Bayan biyan kuɗin fansa, Malamin Jami'a da yan bindiga suka sako ya rasu

Awanni bayan kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane wani Malamin Jami'a ya rasu a kan hanyar zuwa Asibiti.

Lakcaran mai suna, Farfesa Ovaborhene Idamoyibo, ya shiga hannun yan ta'adda ne ranar 9 ga watan Afrilu, suka sako shi ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel