Gwamnatin Buhari ta fara rabon ton 40,000 na hatsi don Easter da Azumi ga talakawa

Gwamnatin Buhari ta fara rabon ton 40,000 na hatsi don Easter da Azumi ga talakawa

  • Ministan Noma, Mahmood Mohammed, ya tabbatar da cewa al'ummar Najeriya na fama da wahalar yunwa
  • Sakamakon haka suka yi gaggawa aiwata umurnin shugaban kasa na bude rumbun hatsi don rabawa mutane
  • Shugaba Buhari ya bada umurnin fitar da ton 40,000 na kayan hatsi don murnar Easter, Azumi da Sallah

Abuja - Ministan aikin noma da raya karkara, Dr. Mohammad Mahmood Abubakar, ya kaddamar da shirin rabon ton 40,000 na kayan hatsi ga talakawa a fadin Najeriya.

Ya bayyana cewa wannan kayan hatsi da aka saki zai rage hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa kuma ya tabbatar da cewa zai kawar da talauci.

A taron kaddamar da rabon kayan hatsin da sansanin yan gudun hijra dake Karmajiji, birnin tarayya Abuja, Ministan yace an fara rabon ne bisa umurnin Shugaban kasa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari

Gwamnatin Buhari
Gwamnatin Buhari ta fara rabon ton 40,000 na hatsi don Easter da Azumi ga talakawa Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, shugaban kasan ya ce a raba ne don murnar bikin Easter, Ramadan da Sallah dake gabatowa.

Dr. Mohammad Mahmood Abubakar yace haka za'a raba kayan dukkan jihohin tarayya.

Yace:

"Gidaje da dama na bukatar taimakon abinci don rage wahalar yunwa da tsadar abinci da suke fama."

Diraktan sashen rumbun abinci, Sule Haruna, yace wannan ita ce manufar ajiyar abincin don rage radadi.

Muna Yabawa Shugaban Kasa Bisa Bude Rumbunan Abinci Saboda Azumi, Sheikh Bala Lau

Kungiyar da'awar addinin Musulunci, Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah JIBWIS, ta jinjinawa shugaban kasan bisa umurnin fitar da hatsi daga rimbun abincin gwamnati.

Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jinjinawa wannan mataki da ya dauka, wanda a cewar sa zai kawo sauki matuka ga al'umma.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafin JIBWIS na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon buhunan abinci kamar yadda Buhari ya bada umarni

Idan ba a manta ba dai, a watan da ta gabata, Sheikh Bala Lau yayi kira na musamman ga shugaban kasa da ya bude rumbunan abinci da asusun gwamnati saboda tallafawa al'umma a cikin watan Ramadaan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel