Bayan biyan kuɗin fansa, Malamin Jami'a da yan bindiga suka sako ya rasu

Bayan biyan kuɗin fansa, Malamin Jami'a da yan bindiga suka sako ya rasu

  • Awanni bayan kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane wani Malamin Jami'a ya rasu a kan hanyar zuwa Asibiti
  • Lakcaran mai suna, Farfesa Ovaborhene Idamoyibo, ya shiga hannun yan ta'adda ne ranar 9 ga watan Afrilu, suka sako shi ranar Lahadi
  • Sai dai yan uwansa sun ɗakko shi rai hannun Allah, suka yi gaggawar kai shi Asibiti don ba shi taimakon farko amma rai ya yi halinsa

Delta - Wani Malami kuma shugaban tsangayar kaɗe-kaɗe na jami'ar jihar Delta. Abraka, Farfesa Ovaborhene Idamoyibo, wanda ya shiga hannun masu garkuwa ranar 9 ga watan Afrilu, 2022, ya mutu.

Punch ta tattaro cewa an ɗakko Farfesan ne cikin mawuyacin hali bayan masu garkuwa sun sako shi biyo bayan karɓan Naira Miliyan N3m a matsayin fansa.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Yan bindiga sun sace Idamoyibo a Eku, ƙaramar hukumar Ethiope ta gabas a jihar Delta yayin da yake kan hanyar komawa Abraka bayan ya halarci taron iyalai a Sapele.

Farfesa a Jami'ar DELSU ya kwanta dama.
Bayan biyan kuɗin fansa, Malamin Jami'a da yan bindiga suka sako ya rasu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Maharan sun buƙaci iyalansa su tattara musu naira miliyan N50m a matsayin fansa kuma sharaɗin da zai sa su sake shi, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa masu garkuwan sun sake shi ranar Lahadi da daddare, amma waɗan da suka je ɗakko shi sun gan shi cikin mawuyacin hali.

Meya faru da Farfesan?

Daga nan, yan uwansa suka yi gaggawar kai shi Asibiti domin ya samu taimakon farko, amma sai aka maida shi Asibitin Koyarwa na Oghara kasancewar rashin lafiyarsa na ƙara tsanani.

Bayanai sun nuna cewa Malamin Jami'ar ya cika ne a kan hanyar zuwa Asibitin Koyarwan kuma Likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa jim kaɗan bayan isa da shi Asibitin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da mutuwar Farfesan bayan kuɓuta daga hannun masu garkuwa.

A wani labarin kuma Babban Malamin Musulunci ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, ya nemi tallafin kuɗi

Wani Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Afeez Akinola na Ibadan jihar Oyo, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari a 2023.

Shehin Malamin ya ce Najeriya na bukatar mutum mai tsoron Allah da zai iya shawo kan matsalolin da suka baibayeta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262