An Tsinci Gawar Ɗan Kasuwar Kano Bayan Iyalansa Sun Biya N6m Ga Masu Garkuwa

An Tsinci Gawar Ɗan Kasuwar Kano Bayan Iyalansa Sun Biya N6m Ga Masu Garkuwa

  • An tsinci gawar Yahaya Hassan Musa, wani dan kasuwa mazaunin Kano a cikin dajin Jihar Kogi bayan yan uwansa sun biya kudin fansa
  • Tun a ranar Alhamis ne masu garkuwa da mutane suka sace Yahaya suka bukaci a biya su Naira miliyan 10 daga baya suka rage zuwa Naira miliyan 6
  • Amma bayan yayansa ya kai wa masu garkuwar kudin a dajin Jihar Kogi, sun kwatanta masa inda zai tafi ya hadu da danwansa amma daga bisani sai gawa aka tarar

Iyalan Yahaya Hassan Musa, dan kasuwa mai shekaru 39, sun shiga zaman makoki bayan an gano gawarsa a wani daji awanni bayan wadanda suka sace shi sun karbi Naira miliyan 6 matsayin kudin fansa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

Lamarin ya samo asali ne a ranar Alhamis, a yayin da mutum wanda ke da aure da 'ya'ya biyu, ke dawowa daga Cotonou, inda ya tafi kasuwanci amma aka sace shi a wani daji da ke Mopa, Jihar Kogi.

An Tsinci Gawar Ɗan Kasuwar Kano a Kogi Bayan Biyan N6m Don Fansarsa
An Tsinci Gawar Ɗan Kasuwar Kano a Dajin Kogi Bayan Biyan N6m A Matsayin Kudin Fansa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa da farko masu garkuwan sun nemi a biya su Naira miliyan 10 domin fansarsa daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 6.

Da ya ke bada labari ga City & Crime, yayan marigayi Yahaya, Abubakar Hassan Musa, wanda ya kai wa masu garkuwan Naira miliyan shidan, ya ce jirgin sama kaninsa ya saba shiga idan ya yi tafiya amma a wannan karon ya shiga mota.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Masu garkuwan sun bukaci in kai musu kudin wani daji da ke Kabba. Na tafi na kai musu kudin. Sai suka min kwatancen inda zan tafi in gan shi amma ban gan shi ba. Ni dai na kwana a daji.

Kara karanta wannan

Duk magidancin cocina da ke dukan matarsa, sai na lakada masa duka, Fasto Suleman

"Na cigaba da nemansa goben ranan har sai lokacin da wata mata da aka sace tare da dan uwa na ta kira ni ta ce sun kashe shi tun kafin su karbi kudin fansar, amma bata san inda suka ajiye gawarsa ba.
"Na tafi wani gari kusa da dajin na dauki hayan mafarauta muka shiga daji don neman gawarsa. Bayan tafiya na kilomita masu yawa, sun tsinci gawarsa ya fara lalacewa."

Ya ce sun gaza samun mota da zai dauki gawar saboda yanayin da suka same shi, sun birne shi bisa koyarwar addinin musulunci a dajin bayan tuntubar yan uwansa a Kano.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya ana gobe daurin aurenta a Kaduna

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164