Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa

Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa

  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya; Chris Ngige ya yi kira ga malaman jami'a karkashin ASUU
  • Ya bayyana cewa, a matsayinsa na uba mai 'ya'ya a jami'o'in Najeriya, yana jin zafin da talakawa ke ji
  • Ya kuma bayyana cewa, aikin gyaran jami'o'in Najeriya na kowa ne ba gwamnati kadai ba, inji sanarwar da ya fitar

FCT, Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya bukaci malaman jami’o’in na ASUU da ke yajin aiki da su duba halin da dalibai da iyaye ke ciki su koma bakin aikinsu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, Ministan ya ce ya kamata malaman jami’o’in su kuma yi la’akari da kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na farfado da tsarin jami’o’i.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

Ngige ya ce Buhari ya yi kokari, ya kamata ASUU ta duba
Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Hakaalika, ya ce ya kamata malaman su su duba irin gaskiyar da gwamnati ta nuna wajen kyautata jin dadinsu kamar yadda yake kunshe a cikin shirin MOA na shekarar 2020.

Jaridar This Day ta naqalto Ngige na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ku yi la'akari da dalibanku da iyayensu; ku yi la'akari da irin hatsarin da wadannan dalibai suke fuskanta a kullum, ba tare da zuwa makaranta ba da kuma damar da aka rasa. Maido da martabar tsarin jami'o'inmu aikin kowa ne kuma gwamnati mai ci ta nuna iya kokarinta.
“A matsayina na uban da ‘ya’yansa ke karatu a jami’o’in gwamnati; Ina jin radadin da talakawan Najeriya ke ji. Don haka ina kira ga ASUU da ta janye yajin aikin yayin da sauran batutuwan da ake takaddama a kai kuma a ci gaba da tattauna su.”

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

Kafin nan, Ngige ya caccaki sharuddan da kungiyar NLC ta bayar, inda ya bayyana cewa tuni gwamnatin tarayya ta kafa tawaga mai karfi da suka hada da shugaban ma’aikata, ministocin kwadago, ilimi, kudi, sadarwa da tattalin arzikin zamani.

Ministan a cikin bayaninsa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya biyan karin 200% na albashin ma’aikatan jami’o’in da tsohon kwamitin sake tattaunawa a karkashin Jubril Munzali ya gabatar ba, kamar yadda Business Day ta kawo.

Ba A Yi Sulhu Da ASUU Ba, NASU Da SSANU Za Su Tsinduma Yajin Aiki Na Sai Baba Ta Gani

A wani labarin, Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC) ta Kungiyar Ma’aikatan Ilimi da Cibiyoyi makamantansu (NASU) da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU), ta bayyana yadda suka shirya tsaf wurin datse duk ayyukansu a jami’o’i da cibiyoyin ilimi da ke fadin Najeriya.

JAC ta nuna alhininta akan yadda gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta wofantar da yarjejeniyar da ta yi da kungiyar akan harkar ilimin kasar nan, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Kakakin JAC, Kwamared Paters Adeyemi wanda ya tattauna da manema labarai a Abuja ya bayyana cewa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.