Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga

Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga

  • Har yanzu basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, Hassan Shamidozhi, na a hannun yan bindigar da suka sace shi
  • Bayan an kai ruwa rana wajen tattaunawa, maharan sun rage kudin fansarsa daga naira miliyan 20 zuwa miliyan 6
  • Sai dai kuma, sun ba iyalansa wa’adin awa 24 su kawo kudin ko kuma su rasa shi a doron kasa

Abuja - Wadanda suka yi garkuwa da Hassan Shamidozhi, basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, sun ba iyalansa wa’adin awa 24 su kawo naira miliyan 6 ko kuma su rasa shi.

Yan bindigar sun yi garkuwa da basaraken ne makonni biyu da suka gabata sannan suka nemi a biya kudin fansarsa naira miliyan 20.

Kara karanta wannan

Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030

An tattaro cewa sun rage kudin zuwa naira miliyan 6 bayan tattaunawa da aka yi da su.

Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga
Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sai dai kuma, a jiya Alhamis, masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar kashe basaraken idan har iyalansa suka gaza hada masu naira miliyan 6 a yau, jaridar The Guardian ta rahoto.

A halin da ake ciki a yanzu, iyalan sun nemi taimakon jami’an tsaro wajen ceto basaraken.

Rundunar yan sandan birnin tarayya bata ce komai kan batun sace basaraken ba

Mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, bata amsa kiran waya ko sakon tes don jin ta bakinta kan lamarin ba, rahoton Daily Trust.

Sai dai ta bayyana cewa an ja hankalin rundunar zuwa ga wani labari mara tushe kuma mai batarwa a wasu bangarori na watsa labarai, musamman a shafukan soshiyal midiya domin haifar da rudani da fargaba a zukatan mazauna birnin tarayya da jama’a gaba daya.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

Ta ce:

“Rundunar na burin watsi da wannan magana mara tushe da kuma tabbatar wa da mutanen yankin cewa tsarin tsaro na rundunar nan da karfinsa kuma ba za a iya yin kutse cikinsa ba a cikin biranen da kewaye."

Ta kuma shawarci mazauna Abuja da su yi watsi da karbar labaran bogi domin hakan ba zai haifar da komai ba face firgici da rashin fahimta a zukatan mutane.

Adeh ta ce rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda a birnin sannan ta bukaci mazauna yankin da su hada hannu da ‘yan sanda domin tabbatar da bin doka da oda.”

Ta kara da cewa:

“Lambobin gaggawa na rundunar ‘yan sandan FCT sune 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883.”

Wadanda suka sace basaraken Abuja sun nemi iyalansa su siyar da gidansa don hada masu miliyan N20 kudin fansa

A wani labarin, mun ji a baya cewa wadanda suka yi garkuwa da basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali ta birnin tarayya sun umurci iyalansa da su siyar da gidansa domin hada naira miliyan 20 da suka bukata na fansarsa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

Daily Trust ta rahoto yadda masu garkuwa da mutane suka farmaki fadar basaraken, Mai Martaba Alhaji Hassan Shamidozhi, a daren ranar Laraba.

Jaridar ta kuma rahoto cewa a lokacin da ta ziyarci garin a ranar Lahadi, wani ahlin gidan basaraken, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutanen sun sha alwashin cewa ba za su sake shi ba har sai sun samu naira miliyan 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel