Gwamna Matawalle ya fallasa wasu manyan mutane dake taimaka wa yan bindiga a Zamfara

Gwamna Matawalle ya fallasa wasu manyan mutane dake taimaka wa yan bindiga a Zamfara

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce akwai sa hannun wasu masu faɗa aji na jihar a taɓarɓarewar tsaro
  • Bisa haka gwamnan ya rantse da Alƙur'ani kuma ya ƙalubalanci sauran shugabannin siyasa su rantse dan kauce wa zargi
  • Ya ƙara jajantawa iyalan mutanen da suka rasa rayuwarsu a lamarin ta'addancin yan bindiga da ya addabi jihar

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya ce manyan masu faɗa aji da mutane ke ganin ƙimarsu na daga cikin masu taimaka wa yan bindiga masu sace mutane a jihar.

Matawalle ya bayyana cewa akwai wasu kwararan hujjoji da ya dogara da su, waɗan da suka nuna mutanen na da hannu a lamarin, kamar yadda Aminiya ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda 'Yan Bindiga Suka Ci Karen Su Ba Babbaka, Suka Halaka Ma'aikacin INEC a Wurin Aikin Rijistar Zaɓe

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar, ya ce bisa dalilin haka ya sa mai girma gwamna ya rantse da Alkur'ani dan tabbatar wa da kuma nesanta kan shi daga zargin hannu a lamarin.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle.
Gwamna Matawalle ya fallasa wasu manyan mutane dake taimaka wa yan bindiga a Zamfara Hoto: thecable/facebook
Asali: Facebook

Ya kuma bukaci sauran mambobin majalisar gwamnatinsa da su bi sahun shi, su rantse da Littafin Allah mai tsarki, Alkur'ani, domin nesanta kan su daga ayyukan yan ta'adda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan haka ya ƙalubalanci baki ɗaya Zamfarawa da yan siyasa da duk wasu masu faɗa aji su ɗauki Alƙur'ani su rantse domin tsame kan su daga zargin alaƙa da yan ta'adda.

Matawalle ya ce:

"Wasu daga cikin waɗan nan mutane masu ƙima ne kuma jiga-jigai da ake ganin girman su (suna taimaka wa yan ta'adda), haka nan akwai masu amsar kuɗaɗe domin kwarmata wa yan bindiga bayanai."

Matawalle ya yi zargin Mahdi Gusau ya gaza Rantsewa

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya ɗaukar wa Yan Najeriya alkawari biyu idan ya zama shugaban ƙasa

Gwamnan ya ce duk waɗan da ke cikin gwamnatinsa sun bi umarninsa sun Rantse, amma tsohon mataimaki, Mahdi Gusau, ya gaza bin matakin domin tsaftace kansa daga zargi.

Gwamnan ya kara jaddada cewa gwamnatinsa ba zata gajiya ba har sai ta ga bayan yan bindiga duk da goyon bayan da suke samu daga wasu bara gurbi.

Daga nan kuma ya ƙara jajantawa iyalan waɗan da lamarin ayyukan ta'addancin yan bindiga ya shafa har suka rasa rayuwarsu, tare da rokon mutanen da aka sace yan uwansu su ƙara hakuri, su amince da matakan da ake ɗauka.

A wani labarin kuma Bayan ganawa da majalisar magabatan ƙasa, Buhari zai sa labule da shugabannin tsaro

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai tattauna da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan ranar Talata mai zuwa.

A ranar Alhamis da muke ci, Shugaban ya gana da majalisar magabatan ƙasar nan da ta ƙunshi shuwagabannin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe Fitaccen ɗan kasuwa har Lahira a gaban Budurwar da zai Aura mako mai zuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel