Dattawan Arewa na jin haushin Buhari ne don ya hanasu mukamai a gwamnatinsa: Fadar Shugaban kasa

Dattawan Arewa na jin haushin Buhari ne don ya hanasu mukamai a gwamnatinsa: Fadar Shugaban kasa

  • Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga dattawan Arewa da suka yi kira ga Buhari yayi murabus
  • Femi Adesina ya ce dattawan Arewan mukami suke so a gwamnatin Buhari, da basu samu ba suka zama yan adawa
  • Kungiyar dattawan Arewa ta ce shugaban kasa yayi murabus daga kujerarsa tun da ya gaza bada tsaro

Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mr Femi Adesina, ya caccaki kungiyar dattawan Arewa da tayi kira ga mai gidansa yayi murabus.

Adesina a jawabin da ya saki ranar Alhamis, ya bayyana cewa lallai akwai matsalar tsaro amma ba Najeriya kadai ke fama ba.

Ya siffanta dattawan Arewan matsayin masu babatu kawai saboda basu samu shiga gwamnatin Buhari ba.

Yace:

"Kungiyar wasu fusatattun yan son rai ne, wadanda suka yi tunanin zasu rika fadawa Shugaba Buhari abinda zai yi lokacin da yayi nasara a 2015."

Kara karanta wannan

Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC

"Musamman wasu daga cikinsu sun yi kokarin gaske don samun mukamai a gwamnati. Da basu samu nasara ba suka zama yan adawa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fadar Shugaban kasa
Dattawan Arewa na jin haushin Buhari ne don ya hanasu mukamai a gwamnatinsa: Fadar Shugaban kasa Hoto: Apc

Adesina ya kara da cewa kowa ya san kungiyar dattawan arewa ta dade tana adawa da gwamnatin Shugaba Buhari, gabani da bayan zaben 2019.

Yace:

"Kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP. Kuma wannan ya riga ya bata musu suna. Kawai siyasa ce, ba wai gaskiya ba."

Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta bukaci murabus din shugaban kasa Muhammadu Buhari nan take sakamakon yawaitar kashe-kashe a fadin kasar nan ballantana arewaci.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daraktan yada labaran kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi wannan kiran a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

Ya ce kungiyar ta mika wannan bukatar ne kuma tana fatan 'yan Najeriya masu tarin yawa za su ji dadin hakan idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbeta.

Ya jajanta kashe-kashe da cin zarafin da ake wa yankuna wanda ya zama ruwan dare kuma a kowacce rana ga 'yan Najeriya. A halin yanzu tafiya ta zama babban hatsari kuma zaman wuri dayan haka yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel