Ministan Buhari ya bai wa wadanda masallaci ya murkushe kyautar N5m a Yobe

Ministan Buhari ya bai wa wadanda masallaci ya murkushe kyautar N5m a Yobe

  • Ministan man fetur, Timipre Sylva ya bada kyautar N5 miliyan ga shugaban Darikar Tijjaniyyah na Nguru dake jihar yobe
  • Kyautar tazo ne bayan rushewar masallacin Sheikh Muhammad Alfathi Gibrima wacce ta lashe rayuka hudu bayan mutane da dama da suka samu raunuka
  • Malamin addinin Islaman ya yi godiya ga ministan bisa mutuntaka da karamcin da ya nuna wa al'umma ba tare da dubi da yare, mukami ko addini ba

Yobe - Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya bada kyautar N5 miliyan ga shugaban Darikar Tijjaniyyah na Nguru dake jihar Yobe, Sheikh Muhammad Alfathi Gibrima.

Tribune Online ta ruwaito cwa, kyautar ta zo ne bayan rushewar da masallacin shi ya yi, wanda ya lashe rayuka hudu, bayan raunata mutane da dama.

Kara karanta wannan

Korarren Liman Nuru Khalid: A da mimbarin masallacin Apo ne cibiyar kamfen din Buhari

Ministan Buhari ya bai wa wadanda masallaci ya murkushe kyautar N5m a Yobe
Ministan Buhari ya bai wa wadanda masallaci ya murkushe kyautar N5m a Yobe. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Sylva ya sanar da batun kyautar ne ta hannun wata babbar gidauniya ga fitaccen malamin addinin karkashin jagoranci shugaban jaridar Dillaliya a Kaduna, Alhaji Ibrahim Gamawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata takarda da mataimakin watsa labaran Gidauniyar, Dr. Musa Muhammad ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana yadda Sheikh Gibrima yayin amsar gudunmawar ya nuna godiyarsa ga ministan a kan irin mutuntakarsa.

Malamin addinin ya kara da cewa, duk da a matsayinsa na Kirista kuma daga Kudancin kasar, Sylva ya nuna alamar hadin kai da jin 'kai wanda sauran 'yan Najeriya ya kamata su yi koyi dashi.

Haka zalika, yayi godiya ga Sylva bisa kirkinsa da kuduri mai kyau ga al'umma ba tare da nuna wani bambamci ba, The Punch ta ruwaito.

"Da sannu za mu cigaba da masa addu'a, gami da masa fatan alkhairi tsawon rayuwarsa. Mun yaba da wannan karamcin, sannan mun gode matuka. Ubangiji kadai zai biyasa."

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Gamawa na siffanta mutuntakar dan siyasan a matsayin mutum mai hangen nesa wanda ke wa kowa fatan alkhairi ba tare da dubi ga yare, mukami ko addini ba.

A cewarsa:

"Ministan man fetur, Timipre Sylva na gabatar da wannan gudunmawar ta N5 miliyan gare ka bayan aukuwar mummunar lamarin na rushewar masallacin, wanda ya lashe rayuka, bayan ya bar mutane da dama da raunuka.
"Yana son mika ta'aziyyarsa ga wadanda suka rasa rayukansu, gami da addu'ar samun sauki cikin sauri ga wadanda suka samu raunuka.
"A matsayinsa na mutum mai tausayi, ya siffanta lamarin a matsayin abun alhini wanda ya cancanci tallafi irin wannan daga garesa.
"A saboda haka ne da kyakyawar niyya ya gabatar da gudummawar sa ga shugaba, wanda ke isar da sakon hadin kai da fahimta tsakanin mutanen mu 'yan Najeriya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng