Sheikh Dahiru Bauchi ya yi buda-baki da tawagar fastocin jihohi 19 na arewa

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi buda-baki da tawagar fastocin jihohi 19 na arewa

  • Tawagar fastocin jihohin arewacin Najeriya 19 sun kai ziyara ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi inda suka yi buda-baki tare a gidansa
  • A karkashin shugabancin Fasto Yohana Buru, fastocin sun bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin kara karfin alaka tsakanin addinai
  • A jawabin Shehin malami Dahiru Bauchi, ya ce ya yi farin cikin ziyarar kuma yana fatan za a cigaba da addu'a ga kasar nan kan halin da take ciki

Kaduna - Tawagar fastocin jihohin arewa 19 sun kai ziyara gidan She`hi Dahiru Usman Bauchi don yi buda-baki da wasu malaman Musulunci da Sheikh din ya karba bakuncinsu.

Aminiya ta ruwaito cewa, Fastocin da suka kai ziyara karkashin jagorancin Fasto Yohana Buru na majami'ar Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, da ke Kaduna sun kai ziyara ga malamin don karfafa alaka tsakanin Kiristoci da Musulmin Najeriya.

Kara karanta wannan

Malaman addini 6 sun rasa rayukansu a hadarin mota a hanyarsu ta dawowa daga da'awa a Kano

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi buda-baki da tawagar fastocin jihohi 19 na arewa
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi buda-baki da tawagar fastocin jihohi 19 na arewa. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC
Fasto Buru ya ce, "Mun kawo ziyarar buda-baki a azumin nan tare da 'yan uwanmu Musulmi gidan Sheikh Dahiru Bauchi ne don inganta fahimta tsakaninmu.
"Sama da shekaru 11 kenan da muke gangamin tabbatar da zaman lafiya musamman a lokutan Iftar don mu kara fahimtar juna da malamai.
“Daga cikinsu har da Muhammad Sa'ad Abubakar, Sarkin Musulmi, Sheikh Ibrahim Zakzaky, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Salihu Mai-Barota da Sheikh Mohammed ibn Abdul na Neja.

A cewarsa:

"Daga cikinsu akwai malami masu makwabtaka da mu irinsu Nijar, Benin duk domin yin wa'azi kan amfanin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninmu."
A karin bayaninsa, "Kirista da Musulmi duk Allah ne mahaliccinsu kuma kowanne addini yana da littafi da aka saukar musu. Dukkanmu 'ya'yan Annabi Adamu ne saboda haka akwai bukatar fahimtar juna."

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari Ya Shiga Jerin Masu Takarar Gwamna a Jiharsa

A yayin jawabinsa, Sheikh Bauchi ya bayyana farin cikinsa da ziyarar da fastocin suka kai masa da kuma kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Ya ce akwai bukatar a cigaba da yi wa kasa addu'a domin samun magance matsalolin da suka yi mana katutu a yanzu. Ya shawarci Kirista da Musulmi da su cigaba da zaman lafiya.

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

A wani labari na daban, babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Dahiru Bauchi.

Tinubu wanda ke neman takarar shugabancin kasar a zaben 2023 karkashin inuwar APC, ya ziyarci Shehin Malamin ne a yayin ziyarar jaje da ya kai jihar Kaduna a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu.

A daya daga cikin hotunan ziyarar tasa wanda tuni suka karade shafukan sadarwa, an gano Tinubu durkushe a gaban jigon na darikar Tijjaniyya yayin da shi kuma ya dafa kansa sannan ya saka masa albarka tare da yi masa tofin addu’o’i.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau

Asali: Legit.ng

Online view pixel