Malaman addini 6 sun rasa rayukansu a hadarin mota a hanyarsu ta dawowa daga da'awa a Kano

Malaman addini 6 sun rasa rayukansu a hadarin mota a hanyarsu ta dawowa daga da'awa a Kano

  • Allah ya yiwa Malaman addini shida da suka tafi da'awa kauye rasuwa a hanyarsu ta dawowa
  • An tattaro cewa daga cikin wadanda suka rasu akwai Sheikh Alkassim, Isiya Tela, Malam Ishaq Rummawa, da Mustapha Musa Sa’ad.
  • Allah ya jikansu da rahama kuma ya kyautata makwancinsu

Kano - Malamain addinin Musulunci masu wa'azi guda shida sun rasa rayukansu a jihar Kano ranar Laraba sakamakon mumunan hadarin mota yayin dawowa daga wajen da'awa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Malaman sun yi hadarin mota ne a hanyar komawarsu gida daga karamar hukumar Sumaila.

Wata jami'in gidauniyar Imam Malik da suka dauki nauyin da'awar ta bayyana cewa sun samu labarin hadarin ne misalin karfe 3 na rana.

Malamain addini 6
Malamain addini 6 sun rasa rayukansu a hadarin mota a hanyarsu ta dawowa daga da'awa a Kano Hoto: Daily NIgerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau

A cewarta, labarin da suka samu shine dukkan Malamai shida dake cikin tawagar da'awar sun rigamu gidan gaskiya.

Ta ce har yanzu ba'a samu bayanai kan sauran wadanda suka raka malaman ba.

Tace:

"Mun taru yanzu a gidauniyar dake unguwar Dakata. Zamu je gidan Sheikh Alkassim Zakariyya don jana'izarsu."

Wasu daga cikin dalibansu sun yi jimamin rashin malaman a shafin ra'ayi da sada zumuntar Facebook.

An tattaro cewa daga cikin wadanda suka rasu akwai Sheikh Alkassim, Isiya Tela, Malam Ishaq Rummawa, da Mustapha Musa Sa’ad.

Shugaba Buhari ya jajantawa tsohon shugaba Jonathan game da mutuwar mukarrabansa

A baya kun ji cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon shugaban Najeriya; Good Ebele Jonathan bisa rashin wasu mukarabbansa biyu a hadarin mota.

Idan baku manta ba, a cikin makon nan ne rahotanni suka karade kafafen watsa labaran Najeriya, inda aka bayyana yadda hadarin mota ya rutsa da tawagar tsohon shugaban kasar a Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

Jim kadan bayan faruwar hadarin, jiga-jigan 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar suka fara aiko da sako jaje da nuna alhini ga Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel