Yan bindiga sun sake kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Anambra, an kashe mutum 1

Yan bindiga sun sake kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Anambra, an kashe mutum 1

  • Yan bindiga sun sake kai hari wani ofishin yan sanda a yankin Oyi da ke jihar Anambra a ranar Alhamis, 14 ga watan Afrilu
  • Sai dai jami'an tsaron sun yi nasarar dakile harin, inda suka kashe daya daga cikin yan bindigar a yayin musayar wuta
  • Sabon harin na zuwa ne kasa da sai’o’i 24 bayan yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda hudu a wani hari da suka kai ofishinsu a jihar a ranar Laraba

Anambra - Yan bindiga sun sake kai farmaki wani ofishin yan sanda a Anambra, kasa da sa’o’i 24 bayan kai hari makamancin haka a jihar.

Rundunar yan sanda a jihar ta ce an kai hari hedkwatar ta da ke Nteje a karamar hukumar Oyi na jihar a ranar Alhamis, 14 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Sabon hari: An sheke dan bindiga yayin da gungunsu suka kai hari ofishin 'yan sanda

A cikin wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya fitar, ya bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 3:00 na tsakar dare.

Yan bindiga sun sake kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Anambra, an kashe mutum 1
Yan bindiga sun sake kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Anambra, an kashe mutum 1 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mista Ikenga ya ce yan sanda sun dakile harin, sannan sun yi nasarar kashe dan bindiga daya a yayin musayar wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa an sanya tsaro a hedkwatar rundunar yan sandan, jaridar Premium ta rahoto.

Kwamishinan yan sandan jihar, Echeng Echeng, ne ya jagoranci yaki da yan bindigar, rahoton The Punch.

Kakakin yan sandan ya ce an kwato makamai, alburusai da layoyi daga wajen yan bindiga.

Har ila yau, ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan ya jadadda shirin rundunar na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

Mista Echeng, ya yaba ma jami’an rundunar kan kokarinsu na fatattakar miyagu daga jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar

Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

A baya mun kawo cewa akalla jami’an yan sanda hudu aka bindige a wani mummunan hari da yan bindiga suka kai kan ofishin yan sanda na Atani da ke karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigar sun kai harin ne a tsakar daren Laraba, 13 ga watan Afrilu.

A cewar wata majiya daga Atani, maharan sun isa yankin ne da misalin karfe 1:30 na tsakar daren Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng