Bacci nake ji: Direban jirgin sama ya ki tuko jirgi daga Legas zuwa Kano saboda gajiya

Bacci nake ji: Direban jirgin sama ya ki tuko jirgi daga Legas zuwa Kano saboda gajiya

  • Direban jirgin Max Air ya ki tuko jirgin saman kamfaninsu daga jihar Legas zuwa jihar Kano saboda ya gaji
  • Rahoto ya bayyana cewa, an ce matukin jirgin ya gaji, kuma bai jin dadi saboda haka bacci zai yi ba tukin jirgi ba
  • Fasinjoji sun fusata, inda suka nemi a mayar musu da kudinsu kawai tun da ba zai yiwu su samu abin da suke so ba

Legas - Fasinjoji sun makale a sashin cikin gida na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas bayan da jirgin Max Air ya gaza tashi kamar yadda aka tsara.

TheCable ta tattaro cewa jirgin na Max Air ADJW7G ya kamata ya bar Legas zuwa Kano ne da misalin karfe 5:20 na yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Ramadan: Magidanci ya lakada wa matarsa mai ciki mugun duka kan abincin Sahur

A cewar Aliyu Muhmeen, daya daga cikin fasinjojin da suka makale da ya zanta da jaridar, an mayar da tashin jirgin zuwa karfe 10 na dare daga lokacin da aka tsara tashinsa saboda wasu dalilai.

Jirgin Max Air ya fusata kwastomomi
Bacci nake ji: Direban jirgin sama ya ki tuko jirgi daga Legas zuwa Kano saboda gajiya | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bayan jiran wasu sa'o'i biyu, da misalin karfe 12 na daren ranar Alhamis, Muhmeen ya ce shi da wasu fasinjoji uku sun tunkari ma'aikacin jirgin na Max Air domin sanin halin da jirgin ke ciki, amma aka shaida matukin jirgin "ya gaji bai da lafiya".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa:

"Mun tunkari ma'aikacin jirgin sai wannan mutumin (ma'aikacin Max Air) ya gaya mana cewa matukin jirgin bai jin dadi kuma ba zai iya sake tashi ba.
“Muna nan muna jira tun karfe 3 na rana domin mu tashi karfe 5 na yamma. Hakan sai da ya ja mu fiye da awa bakwai."

Kara karanta wannan

Abuja ba ta zaman irinku bane: 'Yan sanda sun kama masu sana'ar 'Bola Jari'

Muhmeen ya kara da cewa fasinjojin da suka makale sun haura 60, kuma sun hada da yara da mata.

Masu zuwa Umrah sun makale

Dayawa daga cikin fasinjojin da suka makale, an ce musulmi ne masu azumi, yayin da wasu kuma suka yi shirin shiga jirgin kasa da kasa a filin jirgin saman Kano don tafiya Umrah.

Da suke nuna rashin amincewarsu da jinkirin da aka samu, fasinjojin sun nemi kamfanin da ya mayar musu da kudinsu ko kuma su ajiye su a otal, sannan su sake shirin tafiyar zuwa inda za su tafi a safiyar Alhamis.

Sai dai har zuwa lokacin da muka samu rahoton nan, ba a shawo kan lamarin ba, kuma jirgin bai tashi ba.

Ba wannan ne karon farko da ake samun matsalar tashin jirgi daga kamfanin Max Air ba, kwanakin baya Daily Nigerian ta ruwaito yadda aka samu irin wannan tasgaro a babban binrin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

Jirgin ruwa ya jawo Budurwar da ke daf da aure da mutum 28 sun yi shahada a Ramadan

A wani labarin, mutane 29 aka tabbatar da mutuwarsu a yayin da kwale-kwale ya kife a rafin Shagari a daidai wani kauye da ake kira Gidan Magana a Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta fitar da cikakken rahoto a game da wannan hadari da ya auku a Gidan Magana da ke karamar hukumar Shagari, a jihar Sokoto.

Mafi yawan wadanda suka hallaka a hadarin kananan yara ne masu shekara tara zuwa 17 a Duniya, su na kokarin zuwa kauyen gaba domin su yi itace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.