Za mu bayyana sunayen wadanda suka kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, FG
- Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta yi fallasa tare da bayyana sunayen wadanda suka kai farmakin jirgin Abuja-Kaduna
- Ya tabbatar da cewa gamayyar 'yan Boko Haram da 'yan bindiga ce ta kawo wannan farmakin, ya bukaci 'yan Najeriya su hada kai da gwamnati wurin yakar miyagun
- Bayan kammala taron FEC a Abuja, Magashi ya ce gwamnati za ta yi jawabi ga 'yan Najeriya kan kokarin da take kan farmakin Kaduna da na Jos
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya a jiya ta sanar da cewa nan babu dadewa za ta bayyana sunayen wadanda suka kai farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Gwamnatin ta dora laifin mummunan lamarin da ya faru kan abinda ta kwatanta da gamayyar Boko Haram da 'yan binidga da ke cin karensu a yankin, ThisDay ta ruwaito hakan.
Gwamnatin tarayyar ta ce duk da jami'an tsaro na aiki kan bankado kungiyar da ta kai mugun farmakin, binciken farko ya nuna cewa farmakin gamayya ne tsakanin kungiyoyin ta'addanci, inda aka yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai da gwamnati domin bankado su.
Idan za a tuna, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram da ke aiki tare da wasu 'yan bindigan Kaduna, Zamfara, Sokoto, Niger da Kebbi ne suka kai farmakin.
Amma yayin martani ga tambayoyin manema labarai a karshen taron majalisar zartarwa, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da takwaransa na yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, sun tabbatar da cewa gwamnatin na kan lamarin.
Vanguard ta ruwaito cewa, Magashi yayin amsa tambaya kan ko gwamnati ta san wadanda suka kai farmakin, ya ce:
"A gaskiya ina tunanin shugabannin tsaro na aiki tukuru domin bankado wadanda suka kai harin kuma za su sanar muku da sunansu.
"A kan farmakin Jos da Kaduna, za mu zo mu yi wa jama'a bayani a kan abinda ke faruwa da kuma kokarin da muke yi wurin tabbatar da ta'addancin nan an daina. Muna kan lamarin kuma muna kokari, babu shakka za mu fito lafiya nan babu dadewa."
Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoji na son tattaunawa da 'yan bindiga
A wani labari na daban, ya zama abun azabtarwa da tashin hankali ga iyalan da 'yan bindiga suka yi awon gaba da 'yan uwansu a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan da ya gabata.
Harin ya faru ne a 28 ga watan Maris a dajin Dutse cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, wanda ya lashe rayukan mutane takwas, tare da raunata wasu 26 bayan fasinjoji da dama da suka bace - wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka yi awon gaba da su.
Channels Tv ta ruwaito cewa, bayan sati biyu da batan su, iyalansu na sa ran za su samu 'yanci daga garkuwan da aka yi dasu, duk da sun ki amincewa da neman sasanci da 'yan bindigan.
Asali: Legit.ng