Osinbajo mayaudari ne, ko Yesu zai iya yaudara: Kungiyar Kiristocin Arewa

Osinbajo mayaudari ne, ko Yesu zai iya yaudara: Kungiyar Kiristocin Arewa

  • Wata kungiyar Kiristoci ta yi kira ga shugaban RCCG da yan siyasa su yi hattara da mataimakin shugaban kasa
  • Rabaran Omera ya bayyana cewa Osinbajo ya ki daukan darasin dake cikin littafin Injila kan yaudara
  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinabjo ya ayyana niyyar takarar kujerar shugaban kasar Najeriya

Abuja - Kungiyar Kiristocin Arewa watau Northern Christians Movement (NCM) ta gargadi yan siyasa da Malamai su yi hattara da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Kungiyar tace ta yi hasashen cewa Osinbajo mutum ne wanda zai yaudari duk wanda ya taimakesa.

Wannan ya biyo bayan ayyana niyyar takarar kujerar shugaban kasa da Farfesa Yemi Osinbajo yayi ranar Litinin, rahoton Infong.

Osinbajo
Osinbajo mayaudari ne, ko Yesu zai iya yaudara: Kungiyar Kiristocin Arewa
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

A jawabin da shugaban kungiyar NCM ya saki ranar Litinin, Rabaran Jonah Omera, a Abuja ranar Litinin, yace ayyana ra'ayin takarar da Osinbajo yayi ya nunashi matsayin babban mayaudari, riwayar Solacebase.

Yace:

"Osinbajo wanda ke ikirarin shi Fasto ne na cocin RCCG, yayi watsi da irin alakar da ya gudana tsakanin Apotle Paul da yaron gidansa Timothy, saboda ya bi haka wajen alakar tsakaninsa da maigidansa, Asiwaju Bola TInubu."
"Osinbajo ya yaudari Tinubu kuma ya watsa masa kasa a ido ta hanyar neman kujerar da yake nema."

Rabaran Jonah ya kara da kawai Osinbajo ya dogara ne da kuri'un mambobin cocinsa milyan 12 amma yana gargadin mammalakin cocin RCCG cewa idan ya goyi bayan Osinbajo, shima a kwana a tashi sai ya yaudare sa.

Yace:

"Kamar yadda ake cikin makon da Judas ya yaudari Yesu, haka Yemi Osinbajo zai yaudaru Adeboye yadda ya yaudari Tinubu, saboda halina kenan."

Kara karanta wannan

2023: Muna yi masa fatan alheri, Lawan yace bayan Iftar dinsu da Farfesa Osinbajo

Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta gargadi jam'iyyun siyasa kada su sake su baiwa wani dan cocin Redeemed Church of Christ Group (RCCG) tikitin takara a zabe.

MURIC ta yi wannan gargadi ne a jawabin da shugabanta na shiyar Bauchi, Safiyanu Gambo, ya saki kuma Legit ta samu.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, wanda har yanzu bai bayyana niyyar takararsa ba babban Fasto ne a cocin RCCG.

Ana kyautata zaton cewa nan ba da dadewa ba zai ayyana takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel