2023: Lawan ya bayyana abinda Osinbajo yace wa sanatocin APC, ya sanar da martanin da suka masa

2023: Lawan ya bayyana abinda Osinbajo yace wa sanatocin APC, ya sanar da martanin da suka masa

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya sanar da cewa suna yi wa Yemi Osinbajo fatan alheri
  • Lawan ya sanar da manema labarai cewa, Osinbajo ya sanar da su burinsa na gadar Buhari a Iftar din da suka yi tare
  • A cewar Lawan, sanatoci da 'yan majalisar APC za su cigaba da kokarin ganin jam'iyyarsu ta mulki kasar nan da jihohi har bayan 2023

FCT, Abuja - Sanata Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawa ya ce shi da takwarorinsa suna yi wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo "fatan alheri" a yunkurin sa na zama shugaban kasar Najeriya na gaba, TheCable ta ruwaito.

Osinbajo a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana burinsa na takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

2023: Lawan ya bayyana abinda Osinbajo yace wa sanatocin APC, ya sanar da martanin da suka masa
2023: Lawan ya bayyana abinda Osinbajo yace wa sanatocin APC, ya sanar da martanin da suka masa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

APC Ng Support ta ruwaito cewa, a yammacin Talata, mataimakin shugaban kasan ya karba bakuncin sanatocin APC inda suka yi buda-baki a gidansa da ke fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari

Iftar shi ne cin abincin dare wanda Musulmai ke yi bayan Magriba a watan Ramadan.

An yi cin abincin daren ne yayin wata ganawar sirri.

A yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnatin bayan shan ruwan a gidan mataimakin shugaban kasan da ke fadar shugaban kasa, Lawan ya ce Osinbajo ya bukaci goyon bayan 'yan majalisar ne a kokarinsa na zama magajin Buhari.

Shugaban majlisar dattawan bai bayyana cewa 'yan majalisar za su goyi bayan Osinbajo ba ko a'a.

"Mun yi buda baki tare da mataimakin shugaban kasa, kuma bayan nan mun tattaunawa kan gwamnati da kuma burinsa na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari," Lawan yace.

Ya kara da cewa:

"Mataimakin shugaban kasan ya sanar mana da cewa ya bayyana bukatar sa kuma yana son tuntubar sanatocin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Bayan ganawa da gwamnoni, Osinbajo ya gayyaci 'yan majalisun APC

"Yana son mu ji daga bakinsa kuma mun ji, kuma yana neman goyon bayanmu a kowanne yanayi da za mu iya. Mun yi wa mataimakin shugaban kasan fatan alheri a kan burinsa.
"Amma bari in tabbatar wa da kowa cewa sanatocin APC da dukkan 'yan majalisar tarayya karkashin APC za su cigaba da aiki tukuru wurin ganin cigaban jam'iyyarmu domin ta cigaba da ayyuka ga 'yan Najeriya wurin tabbatar da mulkin APC ne zai cigaba a 2023 har a sauran jihohinmu da izinin Ubangiji APC ne za ta mulke su."

Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari

A wani labari na daban, wasu 'yan Najeriya ba su yi farincikin bayyana bukatar shugabancin kasa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi a ranar 11 ga watan Afirulun 2022.

Mutane da dama ba su yi farin ciki bane saboda kungiyoyin siyasansu ko kuma wasu abubuwa da suka yi imani dasu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mataimakin shugaban ƙasa zai yi buɗe bakin Azumi da Sanatocin Jam'iyyar APC

Masu kiyasi sun ce takarar Farfesa Yemi Osinbajo zata raba kawunan gwamnonin Kudu maso yamma da na jam'iyya mai mulki APC, musamman damar samar da shugaban kasa daga kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel