'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue
- 'Yan bindiga sun kai mummunan farmakin kananan hukumomin jihar Benuwe 3 inda suka halaka basarake da wasu mutum 24
- An gano cewa sun kai harin a daren Litinin kuma sun dinga harbi, hatta wadanda ke gudun ceton rai basu kyale su ba
- Shugaban karamar hukumar Guma ya sanar da cewa tabbas harin ya faru kuma ana zaton makiyaya ne suka kai farmakin
Benue - A daren ranar Litinin ne aka kashe wani basarake, Zaki Unongo Shaayange da wasu mutane 24 a wasu hare-hare uku da 'yan bindiga suka kai yankunan kananan hukumomin Logo, Tarka da Guma, na jihar Benue.
Vanguard ta ruwaito cewa, harin ya bar mutane da dama kwance a asibitoci da raunuka masu tsanani wanda suka samu daga harbin bindiga.
An tattaro daga wani shugaban al’umma, Cif Joseph Anawa, cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai kimanin shida sun tare hanyar Anyiin-Tse Kile a Ukemberagya na karamar hukumar Gaambetiev Logo a daren ranar Litinin da misalin karfe 7:15.
“Sun harbe basaraken gargajiya, Zaki Unongo Shaayange a kauyen Ikyaan, kuma sun kashe wasu da dama yayin da yanzu haka wasu ke cikin mawuyacin hali a Asibitin NKST Anyiin. Daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, Mista Aondoakura Kile ya kuma bayyana cewa, ‘yan ta’addan Fulani sun yi awon gaba da wasu baburan Bajaj na wadanda harin ya rutsa da su,” inji shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazalika an tattaro daga wata majiya mai tushe cewa, a kalla mutane tara ne aka kashe a daren ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 8 na dare a hannun wasu makiyaya da suka kai farmaki kauyen Tse-Sumaka da ke kusa da Umenge, karamar hukumar Mbadwem a karamar hukumar Guma.
Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe
Punch ta ruwaito cewa, ‘yan fashin sun mamaye al’ummar daga makwabciyar jihar Nasarawa, inda suka rika harbe-harbe tare da korar wadanda abin ya shafa daga gidajensu.
“Sun harbe mutane yayin da suke gudu kuma duk wanda suka kama shi bai tsira ba. An kashe mutane tara tare da jigata wasu da dama. A yanzu da muke magana mata da yara suna tserewa daga gidajensu da yawansu don neman wuraren da za su tsira a cikin yankunan da ke makwabtaka,” inji shi.
Da yake tabbatar da harin, shugaban karamar hukumar Guma, Mista Caleb Aba, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa, tabbas harin ya faru.
Ya kara da cewa “a kwanakin nan ba sai an tunzura wadannan Fulani makiyaya ba kafin su kai hari su kashe mu, domin manufar ita ce su kore mu nesa da gidajen magabatanmu, su mallake su.”
An kuma tattaro cewa a daidai lokacin ne makiyayan dauke da makamai suka kai farmaki a kauyen Tiortyu da ke kasa da kilomita 18 daga garin Makurdi, kan hanyar Makurdi-Gboko a karamar hukumar Tarka inda aka yi wa mutane 15 da suka hada da mata kisan gilla.
Wannan harin ya janyo zanga-zangar nuna bacin rai da matasan yankin suka yi. Sun mamaye titin Makurdi-Gboko mai cike da cunkoson jama’a inda suka ajiye gawawwakin wadanda aka kashe na tsawon sa’o’i da dama, tare da dakatar da duk wani motsi da ababen hawa ke yi a wannan yanki na jihar.
'Yan ta'adda sun kone gidan kwamishina, sun hada da na mahaifinsa sun babbake
A wani labari na daban, 'yan bindiga sun babbake gidan kwamishinan shari'a kuma antoni janar na jihar Imo, Cyprian Akaolisa.
Miyagun sun kara da lalata gidan mahaifinsa da ke Obibi, Awo-Idemili da ke karamar hukumar Orsu ta jihar, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Vanguard ta ruwaito cewa, a wata takarda, kwamishinan ya koka kan farmakin inda ya dinga mamakin abinda ya kai 'yan ta'addan gidansa har da na mahaifinsa.
Asali: Legit.ng