'Yan ta'adda sun kone gidan kwamishina, sun hada da na mahaifinsa sun babbake

'Yan ta'adda sun kone gidan kwamishina, sun hada da na mahaifinsa sun babbake

  • 'Yan ta'adda sun kai farmaki gidan kwamishinan shari'a kuma atoni janar na jihar Imo, Cyprian Akaolisa
  • Kwamishinan ya fito inda ya bayyana damuwarsa tare da sanar da cewa miyagun sun hade da gidan mahaifinsa wanda da kanshi ya gina
  • Ya sanar da yadda bata-garin Ibo din suka dauka babbar mota tare da kwashe kayayyakin alatun gidan kafin su murkushe shi

Benue - 'Yan bindiga sun babbake gidan kwamishinan shari'a kuma antoni janar na jihar Imo, Cyprian Akaolisa.

Miyagun sun kara da lalata gidan mahaifinsa da ke Obibi, Awo-Idemili da ke karamar hukumar Orsu ta jihar, Daily Trust ta ruwaito hakan.

'Yan ta'adda sun kone gidan kwamishina, sun hada da na mahaifinsa sun babbake
'Yan ta'adda sun kone gidan kwamishina, sun hada da na mahaifinsa sun babbake. Hoto daga tehcable.ng
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa, a wata takarda, kwamishinan ya koka kan farmakin inda ya dinga mamakin abinda ya kai 'yan ta'addan gidansa har da na mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi

"'Yan kabilar Ibo mutane ne masu kwazo wadanda a cikin shekarun nan suka yi kokari wurin tsara yankunansu tare da habaka su.
"A cikin shekarun da nayi ina gwagwarmaya, na yi kokarin ganin na gina gida saboda iyalina. Mahaifina tsoho ne wanda yayi kokarin gina gidansa da guminsa. A yau dukkan gine-ginen biyu an kone su zuwa toka, 'yan uwana Ibo ne suka kone su.
"Da farko dai, a shekarar da ta gabata an kone garinmu na Obibi da ke Awo-Idemili a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo ba gaira babu dalili. A wannan shekarar an sake dawowa, an kone gidana ko bulo daya ba a bar min ba," a cewarsa.

Kwamishinan cikin kunar rai ya kara da cewa:

"Sai dai a daren jiya, an murkushe gidan mahaifina. Wannan gida ne da mahaifina ya gina da kanshi da kuma gumin shi.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

“Ina son bayyana muku cewa an murkushe tare da lalata gidan da na girma a ciki. Sun fara amfani da babbar mota wurin kwashe dukkan kadarori da suka hada da firji, talabijin, janareto da sauransu.
"Mene ne laifuka na, wa na yi wa laifi? Kuma mene ne laifin mahaifina? Ina sake tambaya, ina halyayyar Ibo din? A yau waye zai zuba hannayen jari a Orsu ana cikin wannan halin?
“Wannan ta'addancin ne ke faruwa a karamar hukumar Orsu? An kone sakateriya baki daya, gidan abokin aikina Chief Prince Ford Ozumba, kwamishinan kwadago da ayyuka na Imo, gidan dan majalisar wakilai ma wakiltar mazabar Orsu da sauran gidajen 'yan siyasa."

Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan Najeriya, rundunar ‘yan sandan Amotekun da ‘Operation Burst’ wacce rundunar hadin guiwa ce ta jami’an tsaro da ta kunshi sojoji da jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence, sun cike dazuzzukan wasu kananan hukumomi uku a garin Ogbomoso na jihar Oyo, domin neman ‘yan ta'addan da ke taruwa a wurin.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa

Punch ta ruwaito cewa, an yi ta rade-radin cewa an ga wani jirgi mai saukar ungulu yana sauka a kan wani tudu a daya daga cikin dazuzzukan yana bayar da makamai da harsasai ga ‘yan fashin da ke taruwa a wurin.

Amma kuma, bayan shafe sa’o’i da dama ana zagaya dazuzzukan ta hanyar amfani da ababen hawa, babura da kuma ‘yan sintiri na kafa da jami’an tsaro suka yi, an tattaro cewa ba a samu wani mai laifi ko ‘yan ta’adda a cikin dajin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel