Zan haramtawa 'yan Najeriya cin nama ganda idan na gaji Buhari a 2023, inji dan takara

Zan haramtawa 'yan Najeriya cin nama ganda idan na gaji Buhari a 2023, inji dan takara

  • Na gaba-gaba a shirin BBNaija, Ebuka Obi-Uchendu, ya jawo cece-ku-ce bayan da ya ambaci abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban Najeriya
  • Shahararren matashin da ake gani a shirin talabijin ya bayyana cewa zai haramtawa iyaye yiwa yara aikin gida tare da haramta cin fatar shanu da aka fi sani da ganda
  • Manufarsa ta takarar shugaban kasa ya nuna ra’ayin cewa Ebuka ba mai son taimaka wa ‘ya’yansa bane wajen aikin gida

Da alama babban mai masaukin baki na shirin Big Brother Naija (BBNaija), Ebuka Obi-Uchendu, bai jin dadin taimaka wa ‘ya’yansa da aikinsu na gida kuma ya yi nuni da hakan a kalamansa.

Ebuka, cikin salo ya bayyana abubuwan da baya son yi kuma ya sanya su cikin jerin abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban kasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

Ma’aikacin gidan talabijin din ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa zai haramtawa iyaye taimakon ‘ya’yansu wajen gudanar da aikin gida nan take bayan ya haramta cin fatar shanu da aka fi sani da ganda.

Mai neman gaje Buhari
Zan hana 'yan Najeriya cin nama ganda idan na gaji Buhari a 2023, inji dan takara | Hoto: @ebuka
Asali: Instagram

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dole ne na haramtawa iyaye taimaka wa 'ya'yansu da aikin gida idan na zama Shugaban kasa. Ya kamata na huta. Nan take bayan na haramta ganda."

'Yan Najeriya sun mayar da martani ga Ebuka kan manufarsa

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun mayar da martani daban-daban game da jerin ayyukan da Ebuka ya gabatar idan ya zama shugaban kasa.

Legit.ng ta dauko wasu daga cikin ra'ayoyin, karanta su a kasa:

Baudex:

"Kar dai ka haramta Dodon Kodi."

Nutraplus_:

"Darussan Verbal da Quantitative sa'anninka ne dama?"

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Bryellan_:

"Ka dai bar ganda ka haramta aikin gida."

Pimp_mygair:

"Ba za ka sami kuri'ata ba idan ka haramta GANDA musamman masu laushi masu kauri daga masu amala."

Doktorfabz:

"Ebuka bai iya aikin gidan quantitative and verbal ba kenan."

Naijatoukmaters:

"Abokina jeka koya musu aikin gida kawai."

2023: Lawan ya bayyana abinda Osinbajo yace wa sanatocin APC, ya sanar da martanin da suka masa

A wani labarin, Sanata Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawa ya ce shi da takwarorinsa suna yi wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo "fatan alheri" a yunkurin sa na zama shugaban kasar Najeriya na gaba, TheCable ta ruwaito.

Osinbajo a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana burinsa na takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

APC Ng Support ta ruwaito cewa, a yammacin Talata, mataimakin shugaban kasan ya karba bakuncin sanatocin APC inda suka yi buda-baki a gidansa da ke fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Facebook, Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel