Soji Sun Ƙwace N60m Da Za A Kai Wa Masu Garkuwa, Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe Ƴan Ta'adda

Soji Sun Ƙwace N60m Da Za A Kai Wa Masu Garkuwa, Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe Ƴan Ta'adda

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kwace kudin fansa mai tarin yawa daga hannun ‘yan bindiga wanda ake zargin kudin fansa ne a Jihar Kaduna
  • Har ila yau, rundunar ta samu nasarar ceto wadanda suka sace ciki har da mata da yara kanana tare da kwace miyagun makamai daga hannunsu
  • An samu bayanai akan yadda wasu da ake zargin jami’an tsaro ne suke cikin masu taimaka wa masu garkuwa da mutanen, kuma yanzu haka suna hannun hukuma

Kaduna - Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kwace makudan kudade wadanda ake zargin kudin fansa ne da aka ba ‘yan bindiga don su saki wasu daga cikin wadanda suka sace a Jihar Kaduna, rahoton Daily Nigerian.

PRNigeria ta tattaro bayanai akan yadda ake zargin wasu jami’an tsaro suna cikin masu kai musu kudin fansar da ake biyansu.

Kara karanta wannan

Mun Bankaɗo Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda

Soji Sun Ƙwace N60m Da Za A Kai Wa Masu Garkuwa, Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe Ƴan Ta'adda
Sojoji Sun Ƙwace N60m Da Za A Kai Wa Masu Garkuwa, Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe Ƴan Bindiga. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar wacce ta samu bayanan sirri ta samu nasarar ceto wadanda aka sace ciki har da mata da yara.

Rundunar sojin sama da na kasa sun hada kai wurin aikin wanda sanadiyyar hakan suka halaka ‘yan bindiga da dama.

Wani jami’in binciken sirri ya sanar da PRNigeria cewa rundunar sojin sama ta 271 da ke Birnin Gwari da kuma rundunar sojin kasa ta FOB a Gwaska ta samu nasarar ceto mutane da dama da masu garkuwa da mutane suka sace.

Za a ci gaba da bincike akan masu kai wa ‘yan bindigan sako

A cewar jami’in:

“An samu kudi tsaba, N60,000,000, man fetur da sauran miyagun makamai yayin da jami’an suka kai musu samame.
“Sauran abubuwan da sojojin suka kwace a hannunsu sun hada da ababen hawa, bindigogi kirar AK-46, magazin da sauran miyagun makamai da wayoyi.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

“Yanzu haka zamu tura masu kai musu sako wadanda jami’an tsaro suka gane, ga rundunar tsaron fararen kaya (DSS) da kuma rundunar tsaro ta binciken sirri, DIA don ci gaba da bincike.”

Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Abuja ba ta zaman irinku bane: 'Yan sanda sun kama masu sana'ar 'Bola Jari'

Asali: Legit.ng

Online view pixel