A Tsige Buhari Idan Bai Zai Iya Samar Da Tsaro Ba, Hakeem Baba-Ahmad

A Tsige Buhari Idan Bai Zai Iya Samar Da Tsaro Ba, Hakeem Baba-Ahmad

- Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci majalisa ta tsige shugaban kasa idan har ba zai iya tsare yan kasa ba

- Ya bayyana haka ne a wani shirin gidan talabijin din AIT Kakaaki ranar Litinin 10 ga watan Mayu

- Ya bayyana wasu karin matakai da za a iya dauka akan masu rike da madafai suka gaza sake nauyin da doka ta dora muusu

Mai magana da yawun kungiyar dattijan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci majalisa da ta tsige shugaba Muhammadu Buhari idan ba zai iya samar da tsaro ga yan kasa ba, rahoton Daily Trust.

Shugaban na fuskantar matukar matsin lamba sakamakon karuwar rashin tsaro a kasar nan.

A Tsige Buhari Idan Bai Zai Iya Samar Da Tsaro Ba, Hakeem Baba-Ahmad
A Tsige Buhari Idan Bai Zai Iya Samar Da Tsaro Ba, Hakeem Baba-Ahmad. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

Da yake magana a shirin Kakaaki, na gidan talabijin din AIT, ranar Litinin, Baba-Ahmed ya bukaci masu rike da mukamai da su fahimci halin da kasar nan ke ciki, su kuma yi wani abu na daukar mataki ba wai daukar alkawarurruka ba.

DUBA WANNAN: Wani Mutum Ya Kutsa Wurin Casu Ya Bindige Mutum 6 Ciki Har da Budurwarsa

"Hanya daya da muke da ita shine yan majalisu su bibiya ayyukan wannan gwamnati, su fahimci inda shugaban kasa ya gaza, su fahimci inda ba wata hujja da za ta nuna cewa ana yin wani abu don daukar mataki, sannan su duba kundin tsarin mulki wanda yace babban aikin gwamnatin shine tsare rayuwar yan kasa da kuma tabbatar da walwala da jin dadin su."

"Idan Buhari ya gagara haka, ni a gani na, in ya gaza haka a tsige shi. A wata shida da suka gabata, ko shekara biyu, me shugaban kasa ya yi don tsare kasar? Maganar gaskiya ba abun da aka yi sai dai ma koma baya wajen tsare rayuwar al'umma," a cewar sa.

"Ko kuma, kamar yadda tsarin dimokradiyya ya bada dama, masu alhakin tsigewa, su shige wanda suka gaza. Idan shugaban kasa ya gaza a tsige shi.

"Bamu da yan majalisu masu kishin kasa fiye da wasu tsirarun yan siyasa bare su gane cewa idan suka gaza, suma sun gaza.

"Rashin iya mulki ya janyo mutanen da muka zaba muka aika Abuja suke tunanin su yi wa shugaban kasa aiki ba yan kasa ba."

KU KARANTA: An Kama Hatsabibin Ɗan Shekara 30 Da Ke Yi Wa Mutane Fyaɗe a Sokoto

A cewar Baba-Ahmad, mataki na biyu shine yan kasa su taru su yanke matakin da ya kamata su dauka.

Ya ce mataki na uku shine: "shugabannin da suka gane gazawar su da kansu suka san sune matsalar, suyi murabus da kansu saboda basu da abin da su iya a shugabanci.

Baba-Ahmed yayi maganar ne kwana kadan bayan fadar shugaban kasa tace wasu manya na son chanjin gwamnati.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel