Sai dai kai ka zo: Tinubu ya tura gayyata ga gwamnonin APC, suka ki amsa gayyatarsa

Sai dai kai ka zo: Tinubu ya tura gayyata ga gwamnonin APC, suka ki amsa gayyatarsa

  • Majiya mai tushe ta bayyana yadda gwamnonin APC suka ki amsa gayyatar da Bola Tinubu ya yi musu zuwa gidansa da ke Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa, Tinubu ya yi gaggawar gayyatar gwamnonin ne bayan ganawarsu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi
  • Tinubu da Osinbajo na daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka hada da Chibuike Amaechi da Dave Umahi

Majiya mai tushe daga APC ta bayyana yadda gwamnonin APC suka yi watsi da gayyatar da Tinubu inda suka dage cewa tsohon gwamnan na jihar Legas shi dai ya ziyarce su domin baje kolin ra’ayoyinsa a matsayinsa na dan takara a zaben 2023 mai zuwa.

A cewar rahoton da jaridar Authority ta fitar, gwamnonin sun yi biris da yunkurin da Tinubu ya yi na jawo gwamnonin zuwa gidansa na Asokoro.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Maimakon gwamnonin su amsa gayyatar, sai suka nemi ya zo masaukin gwamnan jihar Kebbi domin ya yi shawara da su.

Yadda ta kaya tsakanin gwamnonin APC da Tinubu
Sai dai kai ka zo: Tinubu ya tura gayyata ga gwamnonin APC, suka ki amsa gayyatarsa | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC.

Gwamnonin sun gana da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, SAN a ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu, kwana guda kafin ya bayyana aniyarsa ta maye gurbin maigidan sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majiyar da aka ruwaito a cikin rahoton ta cewa:

"Wannan yana nuni da wanda ake gani a matsayin wanda babu tantama shi ne a kan gaba kuma mai yiwuwa ya fi shahara a cikin 'yan takara."

Majiyar ta ci gaba da cewa ganawar da gwamnonin APC suka yi da Tinubu washegarin da suka gana da mataimakin shugaban kasar a gidansa, ba komai bane face irin ganwarsu da Osinbajo a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Osinbajo ya tara gwamnonin APC don shaida musu aniyarsa ta gaje Buhari

Har yanzu dai ba a bayyana ko gwamnonin za su gana da wasu masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a bainar jama'a ba.

Sauran ‘yan takarar da ke kan gaba a jam’iyyar su ne ministan sufuri; Chibuike Amaechi, gwamnan jihar Ebonyi; Dave Umahi, tsohon gwamnan jihar Imo; Sanata Rochas Okorocha, da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Wani rahoto da jaridar BusinessDay ta buga na nuni da cewa, Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar APC, ya fara tuntubar jam’iyyar SDP, a matsayin wata hanyar da zai bi wajen tabbatar da aniyarsa ta gaje Buhari, idan APC ta kasa ba shi tikitin takara.

A cewar rahoton, majiyoyi na kusa da SDP sun ce Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar a kwanan baya domin neman ma kansa masaukin siyasa.

Matakin da Tinubu ya dauka, an ce ya samo asali ne sakamakon lamarin da ya kai ga fitar da ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar APC da wasu mukamai a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Wani jigo a jam’iyyar APC a cikin rahoton ya ce:

“Tinubu ba zai bar komai haka kawai ba yayin da ake ci gaba da rububin siyasa a tsakanin manyan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki."

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a watan Disamban 2021 ya yi magana kan yadda ya zama mataimakin shugaban kasa a APC a 2015.

Bidiyon da ya saki ya bayyana a watan Janairu a Twitter yayin da ake ta rade-radin cewa Osinbajo na son gaje kujerar Ubangidansa Buhari a 2023, faston kuma farfesan shari'ar ya alakanta zamansa mataimakin shugaban kasa da ikon Allah.

Binciken da Legit.ng ta yi ya nuna cewa mataimakin shugaban kasa ya yi magana kan matsayinsa ne yayin da ya ziyarci Rabaren Udochi M Odikanwa a taron gangamin Restoration Life Assembly International da aka yi a watan Disamban 2021.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.