Kano: Gwamna Ganduje ya sake sabbin nada-nade masu muhimmanci a jihar Kano
- Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi sabbin nada-nade a ma'aikatar gwamnatin Kano
- Ya nada sabbin sakatarorin dindindin da kuma shugaban ma'aikata na jihar inji wata sanarwar gidan gwamnati
- A bangare guda, gwamna Ganduje ya bayyana cewa, jajircewa da kwarewarsu ce ta kawo su matsayin da ya basu
Jihar Kano - Wani rahoton jaridar The Nation ya ce, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya amince da nadin Malam Usman Muhammad a matsayin shugaban ma'aikata na jihar (HoS).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Mista Abba Anwar ya fitar jiya a Kano.
Anwar ya ce gwamnan ya kuma amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda hudu a ma’aikatar gwamnatin jihar.
Ya ce Muhammad ya kasance babban sakatare a ma’aikatar yada labarai kafin nadin nasa a matsayin shugaban ma'aikata.
A cewar Anwar:
“Sabbin Sakatarorin Dindindin din sun hada da Muhammad Shehu, wanda har zuwa lokacin da aka nada shi, shi ne Daraktan Bincike da Kididdiga na Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar (KARMA).
“Sauran su ne Malam Magaji Lawan wanda shi ne Daraktan kudi da asusu na ma’aikatar kudi kafin nadin sa.
“Saura biyun su ne Mista Bilyaminu Zubairu, da Malama Mairo Dambatta'"
Yace nade-naden nan take za su fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
Ganduje ya taya su murna
Yayin da yake taya su murnar samun sabbin mukaman nasu, gwamna Ganduje ya ce su yi koyi da kyawawan halaye a aikin gwamnati, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A kalaman ganduje:
"Dole ne ku dauki yin amfani da dabarun tushen IT a cikin ayyukan ku na yau da kullum azaman wani bangare na hakkin da ke kanku.
"Dole ne kuma ku tuna cewa, tabbatattun halayen ku ne suka kai ku zuwa wannan matsayi. Don haka duk idanu za su kasance a kanku don ganin rawar da za ku taka.”
Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31
A wani labarin, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a kan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) wajen lashe dukka kujeru 31 a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar.
Babban sakataren hukumar zabe ta jihar, Alhaji Lawal Faskari ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu a garin Katsina.
Faskari ya kuma bayyana cewa ba a kammala zabe ba a kananan hukumomin Daura da Funtua, PM News ta rahoto.
Asali: Legit.ng