Matashin Najeriya yace zai samar da Amala da nama, tsire da giya a kyauta idan ya zama shugaban kasa

Matashin Najeriya yace zai samar da Amala da nama, tsire da giya a kyauta idan ya zama shugaban kasa

  • Matashin ya janyo cece-kuce a Twitter bayan ya sanar da burinsa na zama shugaban kasa da kuma ababen arzikin da zai dinga yi wa kasa
  • A cewar matashi Ayo, zai samar da amala da naman akuya kyauta, tsire da giya duka kyauta jama'a za su dinga samu
  • Ya sanar da cewa, a zabe shi domin kuwa beraye za su yi kuka kamar beraye, tsuntsaye kamar tsuntsaye sannan dan Adam kamar mutum

A yayin da 'yan siyasan Najeriya ke cigaba da fitowa suna bayyana ra'ayinsu na neman kujerar shugabancin kasa, wani matashin dan Najeriya mai suna Ayo FBI a Twitter ya sa mabiyansa nishadi da dariya kan kalamansa na kamfen idan an zabesa shugaban kasa.

Kamar yadda ya bayyana, idan har aka zabesa, komai zai tafi daidai. Ayo wanda ya bayyana hakan a wallafarsa mai ban dariya yace:

Kara karanta wannan

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

Matashin Najeriya yace zai samar da Amala da nama, tsire da giya a kyauta idan ya zama shugaban kasa
Matashin Najeriya yace zai samar da Amala da nama, tsire da giya a kyauta idan ya zama shugaban kasa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

"Da tsananin kankan da kai da kuma fatan samun tsananin goyon bayan Ubangiji da ku baki daya, ina sanar da ku niyyata ta neman kujera mafi daraja ta kasar nan; ofishin shugaban kasar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yayin mulkina a matsayin shugaban kasar Najeriya, beraye za su yi kuka kamar beraye, tsuntsaye za su yi kuka kamar tsuntsaye, dan Adam zai yi kamar mutum.

1. Tsire zai zama kyauta ga kowa.

2. Amala da naman akuya za su zama abincin dukkan 'yan Najeriya.

3. 'Yan Najeriya sun daina siyan abinci, abinci zai zama kyauta ga kowa.

4. Duk wani dan jam'iyyata da ya zabe ni, ba zai sake siyan giya ba. Zan tirsasa duk kamfanonin giya na kasar nan su dinga yi kyauta.

A martanin wasu daga cikin mabiyansa da suka nishadantu da kalamansa, sun yaba masa matuka. Ga wasu daga cikin yabon da ya samu.

Kara karanta wannan

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

AbdulMuiz ya rubuta: "Ba mu da lokaci, mu gana da karfe 12 na daren yau domin tattaunawa kan tsarikanmu da dabarun shiga kauyuka, kasuwanni, gidajen marayu da kuma wasu zababbun 'yan siyasa domin mu dauka hoto. Mutum ne shi na mutane, 2023 ta mu ce."

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Azeez ya fara aikin dafa shinkafar dafa-duka irin ta Najeriya a titin Landan, wanda yasa Turawa da dama suka yaba da irin dadin abincin. A hoton da @IamOlajideAwe ya wallafa, anga wasu turawa na layin siyan abincin a gidan saida abinci.

Yayin hira a kafar sada zumunta da wakilin Legit.ng, Azeez ya bayyana yadda ya fara gudanar da siyar da abincin tare da wani, amma yanzu shi kadai ke gudanarwa.

Azeez ya ce: "Ni dan Legas ne daga Surulere. Muna zama ne a Landan, saboda haka muka yanke shawarar kawo abincin cikin birnin. Mu biyu muka fara, amma yanzu da kaina nake yi."

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng