2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi
- A shirinsa na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya fara da neman shawarwarin sarakunan gargajiya
- Amaechi ya ziyarci sarakunan Bichi, Kano da na Daura inda ya nemi albarkarsu kan burin da yasa gaba na shugabancin kasa
- Ya sanar da cewa nan da watan Satumba jami'ar Daura ta sufuri za ta fara aiki kuma hakan zai amfani jama'ar Daura ba kadan ba
Kano da Daura - Ministan sufuri, Honarabul Chibuke Rotimi Amaechi a ranar Litinin, ya ziyarci sarakunan Kano da Daura domin burinsa na fitowa takarar shugabancin kasa.
Wannan ziyarar na zuwa ne bayan kwanaki biyu da ministan ya bayyana burinsa na fitowa takarar shugaban cin kasa a 2023.
Ya ziyarci sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da takwaransa na Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, a fadarsu inda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Yayin yi masa maraba a fadar, sarkin Kano ya mika godiyarsa ga ministan da ya zai jihar Kano a karon farko na ziyararsa.
"Na san shi tun lokacin yana kakakin majalisa har zuwa lokacin da ya zama gwamna yanzu kuma ga shi minista. Jama'a sun san irin rawar da ya taka a baya da kuma yanzu. Duk wadannan abubuwan sun zama tsanin da ya dace ya nemi takarar shugabancin Najeriya," sarkin yace.
A bangarensa, sarkin Bichi ya ce ya dade da tsohuwar alaka da ministan kuma yana fatan kasar nan za ta samu shugabanci nagari, Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi kira ga dukkan 'yan takara da shugabannin yanzu da su saka kasar nan farko a duk halin da suka tsinci kansu.
"Muna maraba da minista zuwa masarautar Bichi kuma muna masa fatan alheri. Muna fatan samun shugabanci nagari tare da fatan zabe na gaba zai kasance cikin lumana."
A Daura, garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministan ya duba ginin jami'aar sufuri.
Ya ce jami'ar za taa faraaiki a watan Satumba inda ya ce an ka matakin kasshe naa ginin.
A fadar Mai Maartaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ministan ya sanar masa amfanin da jami'ar za ta ka masarautar.
Ya ce da yawa daga cikn 'yan Daura za a horar da su tare da ba su aiki a jami'ar. Ya bukaci albarkarsa kan burinsa na zama shugaban kasa, kuma ya samu.
Ku Bani Kuɗi Kawai, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Na Ke So Ba, Amaechi Ya Faɗa Wa Magoya Bayansa
A wani labari na daban, ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya ke karyata jita-jitar cewa zai fito takarar shugaban kasa a 2023, ya bukaci magoya bayansa su bashi kudi a maimakon kujerar shugabancin kasar.
Idan za a tuna, The Punch ta rahoto cewa wata kungiya, Amaechi Vanguard a Amurka da Canada, ta bukaci jam'iyyar na APC ta zabi Amaechi a matsayin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a 2023.
Asali: Legit.ng