Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah a Abuja

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah a Abuja

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun bindige Adamu Aliyu, shugaban kungiyar Miyetti Allah a yankin Gwagwalada da ke birnin tarayya Abuja
  • Maharan sun kashe Aliyu ne tare da wasu mutane hudu a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Izom da ke jihar Neja, inda suka je siyar da shanaye
  • Yan bindigar sun fito ne daga wani jeji inda suka bude masu wuta, yanzu haka wasu mutane uku na asibiti suna jinya sakamakon rauni da suka samu

Abuja - Yan bindiga sun farmaki yankin Gwagwalada da ke Abuja, inda suka bindige shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin, Adamu Aliyu, har lahira.

An tattaro cewa yan bindigar sun kashe Adamu Aliyu ne tare da wasu mutane hudu a kusa da kauyen Daku a gudunmar Dobi da ke yankin a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

Daily Trust ta rahoto cewa sakataren kungiyar MACBAN, Mohammed Usman, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Lahadi, ya ce an yi garkuwa da mutane uku, yayin da wasu uku da suka jikkata ke karban magani a asibitin koyarwa na Gwagwalada.

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah a Abuja
Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah a Abuja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce lamarin ya afku ne a ranar Alhamis da ta gabata da misalin karfe 5:00 na yamma, lokacin da suke a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Izom da ke jihar Neja a babbar motar Dyna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindigar sun fito fito ne daga wani jeji sannan suka budewa motar wuta.

A cewarsa yan bindigar sun tarwatsa gilashin babban motar, wanda ke dauke da marigayi shugaban na MACBAN da wasu fasinjoji.

Ya ce:

“Suna dawowa daga kasuwar Izom da ke jihar Neja ne inda suka je siyar da shanaye, saura masu kilomita daya zuwa kauyen Daku sai yan bindiga suka bayyana daga jeji sannan suka budewa motar wuta, inda suka kashe shugaban MACBAN da wasu mutane hudu.”

Kara karanta wannan

Wasu barayi sun sace gadar karfe mai tsayin kimanin mita 20 a kasar Indiya

Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a matsayin Saleh, Aliyu, Muhammadu da Saidu, cewa an binne gawarwakin mamatan daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Daily Trust ta rahoto cewa jami’an tsaron hadin gwiwa da suka hada da sojoji, civil defence, yan sanda da yan banga karkashin jagorancin kwamandan yan sanda Gwagwalada sun je kauyen Daku, kafin a binne mamatan.

Shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Adamu Mustapha, ya tabbatar da lamarin ta wayar tarho, sai dai bai yi Karin haske ba domin yace yana a cikin wata ganawa.

Zuwa yanzu ba a ji ta bakin kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine ba.

‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama

A gefe guda, wani rahoton da jaridar Punch ya fitar ya ce, wasu 'yan ta'adda sun yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya

karkashin karkashin "Following “ don samun labaran Legit.ng a shafinka na Facebook akai-akai Rahoton ya tattaro cewa, an ce ‘yan ta’addan sun kai farmaki a unguwar Daza da ke karamar hukumar Munya ta jihar, inda suka yi ta harbe-harbe ba kakkautawa.

Mazauna garin da dama sun tsere daga yankin sakamakon harin da aka kai a daren jiya Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng