NDLEA ta kama sinkin hodar iblis 101 a cikin bargunan yara a Legas

NDLEA ta kama sinkin hodar iblis 101 a cikin bargunan yara a Legas

  • Hukumar yaki da fasa-kabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta damke hodar Iblis mai nauyin 13.2Kg a filin sauka da tashin jiragen sama na Legas
  • An kama wani dan asalin jihar Imo mai suna Uchenna Hillary da miyagun kwayoyin da ya boye a cikin bargunan kananan yara
  • Uchenna wanda ya dawo daga kasar Brazil, ya bayyana cewa an biya shi N5 miliyan in har ya kai kwayoyin inda aka umarta a jihar Legas

Legas - Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu sunki 101 na hodar Iblis da aka boye a bargon yara a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, wanda ya tabbatar da kamen ta wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a shafin hukumar na Twitter, ya ce miyagun kwayoyin sun samu shigowa kasar nan ta hanyar wani dattjo mai shekaru 52 da ke dawowa daga kasar Brazil.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

Wanda aka kama da miyagun kwayoyin mai suna Akudirinwa Hilary Uchenna, dan asalin karamar hukumar Oru ta gabas ne da ke jhar Imo.

NDLEA ta kama sinkin hodar iblis 101 a cikin bargunan yara a Legas
NDLEA ta kama sinkin hodar iblis 101 a cikin bargunan yara a Legas. Hoto daga @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Uchenna ya shiga hannu a ranar Asabar a dakin saukar matafiya da ke filin sauka da tashin jiragen sama bayan dawowarsa daga Sao Paulo, Brazil ta jirgin Qatar Airline.

An samu sunki 101 na hodar Iblis din mai nauyin 13.2Kg boye cikin kayan shi yayin da ake duba matafiya.

"A yayin tattaunawar farko, Uchenna, wanda yayi ikirarin cewa shi kafinta ne, ya bayyana cewa an biya shi kudi har N5 miliyan domin safarar kwayoyin kuma ya kai su har inda aka bukata a Legas," Kakakin NDLEA ya sanar.

NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin 374.397kg daga masu safara a jihar Kano

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), a jihar Kano ta bayyana yadda ta kama wiwi mai nauyin kilo 374.397, da wasu mutane 131, wadanda ake zargin su da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, 2022.

Kwamandan NDLEA na jihar, Abubakar Idris Ahmad, ya bayyana hakan ne a Kano yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba.

Ya ce, an damko wadanda ake zargin a wurare daban-daban a cikin jihar, bayan tsananta bincike da jami'an rundunar suka yi, inda ya kara da bayyana yadda wadanda ake zargin suka kunshi maza 125 da mata shida.

Kwamandan ya ce, hukumar ta kama wiwi mai nauyin kilo 374.397; Codeine mai nauyin kilo 1.3, Diazepam mai nauyin kilo 189.585, 100g na Raphenol da sauran haramtattun abubuwa cikin lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel