Ya taro 'Match': Bidiyon tashin hankali yayin da mai tura kuran ruwa ya kwarzane mota Benz

Ya taro 'Match': Bidiyon tashin hankali yayin da mai tura kuran ruwa ya kwarzane mota Benz

  • Wani mai tura ruwa ya yi amfani da kurarsa ya fasa wata mota mai tsada kirar Mercedes Benz a tsibirin Victoria da ke Legas, inda nan take ya haifar da wani yanayi
  • An yada faifan bidiyon da ke nuna dandazon jama'a yayin da suka taru don ganin yadda za su sasanta lamarin cikin lumana
  • Mutane da dama a soshiyal midiya sun yi ta yada bidiyon Instagram, inda da yawa daga cikinsu ke rera waka mai suna "You don bash my car oyinbo rekpete" ga mai tura ruwan

Cikin rashin sani, wani mai tura ruwa a kura ya yi amfani da kurarsa wajen yiwa wata mota kirar Mercedes Benz mai tsada a Legas illa.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a wani wuri a tsibirin Victoria, a cewar wani faifan bidiyo da aka gani a Instagram.

Kara karanta wannan

Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

Yadda mai tura ruwa a baro ya taro rikici
Ya taro 'Match': Bidiyon tashin hankali yayin da mai tura kuran ruwa ya kwarzane mota Benz | Hoto: @instablog9ja and Getty Images/Jean Chung
Asali: UGC

Jama'a sun taru domin sasanta lamarin

Wannan lamari mai sarkakiya ya jawo hankalin masu wucewa yayin da suke kokarin ganin yadda za a daidaita lamarin ba tare da tashin hankali ba.

Sai dai ga dukkan alamu lamarin bai zo da sauki ba domin wata murya a cikin faifan bidiyon ta tambayi ta yaya mai tura ruwan zai samu kudin gyara barnar da ya aikata. Ba a dai sani ba ko daga baya mai motar ya yafe wa mutumin ba.

'Yan Najeriya a shafin Instagram sun yi martani

A halin da ake ciki, 'yan Najeriya sun shiga sashin sharhi na faifan bidiyo da @instablog9ja ya yada a Instagram.

Ga kadan daga cikin abin da suke fada a kasa:

@investorandrew_ ya ce:

"Ina fatan mai wannan benz din bai karbi ko kwabo daga wurin mutumin ba."

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

@victoria_beth yayi sharhi da cewa:

"Ba a yaki da irin wannan abu, ka sasanta lamarin kawai ka koma gida."

@domingo_loso ya mayar da martani:

"Babu dama, haka suke amfani da kura sakaka kawai."

@ronkeyzee yace:

"Lagos ce ainihin ma'anar abin da ake nufi matsala ba ta karewa."

@mizzdebs ya ce:

"Haka meruwa yake. Kullum suna goga kafada da motoci akan hanya."

Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

A wani labarin, farin cikin wani dan Najeriya ya koma nan take bayan da ya fasa asusunsa da zimman ganin kudi amma ya ga sabanin haka.

Mutumin da ke cikin rudani ya samu fararen takardu a madadin kudaden da yake adanawa mafi karancin daraja kamar N5, N10 da N20.

Cikin kaduwa da abin da ya samu a asusun ajiyarsa na katako, mutumin ya dauki bidiyon lamarin, wanda @instablog9ja ya yada a Instagram.

Kara karanta wannan

Maganin kiriniya: Bidiyon kakan da ya danna jikansa a bokiti ya jawo cece-kuce a intanet

Asali: Legit.ng

Online view pixel