Kuma dai, Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna

Kuma dai, Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna

  • Shugaban yan sandan Najeriya karo na biyu ya koma hanyar Abuja-Kaduna don tabbatar da tsaro
  • IGP Alkali yace yanzu an tura jirage masu saukar angulu sintitri a titin don taimakawa yan sanda
  • Makon da ya gabata, IGP Alkali ya bayyana cewa an zuba karin jami'an tsaro don bada tsaro a hanyar

Kaduna - A ranar Asabar, Sifeto Janar na yan sandan Najeriya, IGP Usman AlkaliBaba, ya sake komawa sintiri babban titin Abuja-Kaduna domin duba jami'an tsaron da ya zuba don tabbatar da tsaro.

IGP Alkai ya tafi sintirin ne bayan halartan daurin auren diyyar Gwamnan jihar Delta a Cocin tarayya dake Abuja ranar Asabar, 9 ga Afrilu, 2022.

Ya umurci rundunar yan sandan sama sun zurfafa sintirin sama a hanyar da cikin garin Kaduna don taimakawa rundunar kasa don neman bayanan leken asiri.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Sifeto Janar IGP
Kuma dai, Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakana jawabin da ya saki da yammacin nan.

A cewarsa, IGP ya jaddada niyyar tabbatar da isasshen tsaro a fadin tarayya don jin dadin al'umma.

Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro

Makon da ya gabata mun kawo muku cewa Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Usman Alkali, ya jagoranci sintiri na musamman zuwan titin Abuja zuwa Kaduna ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, 2023.

IGP Alkali tare da dinbin jami'an yan sanda sun dira titin da tsagerun yan bindiga suka addaba don ganin abin da ke gudana.

Prince Olumuyiwa Adejobi yace IGP Alkali ya baza jami'an tsaro masu muggan makamai don tabbatar da tsaro titin.

Kara karanta wannan

An Kai Wa Ɗan Takarar Gwamna Da Tawagarsa Hari, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng