Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Dakarun Ruwan ISWAP, Abubakar Ɗan-Buduma Da Mayaƙansa 19

Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Dakarun Ruwan ISWAP, Abubakar Ɗan-Buduma Da Mayaƙansa 19

  • Sojojin Hadin gwiwa na kasashen da ya yaƙi da Boko Haram, MNJTF, sun yi nasarar kashe kwamandan ISWAP, Abubakar Ɗan-Buduma
  • Dakarun na MNJTF sun halaka Abubakar Ɗan-Buduma da wasu mayaƙansa 19 ne a harin sama da kasa da suka kai musu
  • Abubakar Ɗan-Buduma shine babban kwamandan mayaƙan ISWAP na ruwa da ke kula da yankuna da dama a ƙaramar hukumar Marte

Borno - Dakarun hadin gwiwa na kasashe hudu da ke yaki da Boko Haram, MNJTF, a harin sama da suka kai sun kashe Abubakar Dan-Buduma, babban kwamandan ISWAP da wasu mayaƙa 19 a yankin Tafkin Chadi.

An kashe Dan-Buduma da sojojinsa ne a wani harin da aka kai na sama da kasa da dakarun na MNJTF suka kai a kauyen Kwalaram, ƙaramar hukumar Marte, Jihar Borno, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Nasrun minAllah: Boko Haram sun sheƙe kwamandojin ISWAP 10 a yankin tafkin Chadi

Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Dakarun Ruwan ISWAP, Abubakar Ɗan-Buduma Da Mayaƙansa 19
Sojojin MNJTF Sun Kashe Babban Kwamandan Dakarun Ruwan ISWAP, Abubakar Ɗan-Buduma Da Mayaƙansa 19. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A Janairun 2022, PRNigeria ta rahoto cewa ISWAP ta yi canjin shugabannin ta bayan an kashe wasu kwamandojinsu a harin sama.

Wasu cikin wadanda aka naɗa ɗin sun hada da Dan-Buduma don sa ido kan Bakkassi Buningil da Doron Buhari; Muhammad Ba'ana ya mulki Kirta; Mohamet Aliamir ya kula da Kwalaram; Bukura Gana ya mulki Jubularam; Malam Musa shima Jubularam; sai Mohamadu Mustapha kuma Marte.

Abubakar Dan-Buduma, wanda ya maye gurbin Muhammad Ba'ana, shine babban kwamandan mayaƙan ruwa na ISWAP a Kirta, Bakassi, Buningil da Doron Buhari a ƙaramar hukumar Marte na Jihar Borno.

Sojojin Najeriya Sun Sheƙe 'Yan Ta'adda 80 a Arewa Maso Tsakiya: DHQ

A wani rahoton, Hedkwatar rundunar tsaro da ke Abuja ta bayyana yadda dakarun soji suka samu nasarar halaka ‘yan ta’addan akalla 80 cikin makwanni biyu a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufa'i ya yi gaskiya, hanya ɗaya ce ta kawo karshen yan ta'adda, Tinubu ya magantu

Darektan labaran sojin, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai dangane da ayyukan da sojojin suka aiwatar tsakanin ranar 25 ga watan Maris zuwa ranar 7 ga watan Afirilu a ranar Alhamis a Abuja.

A cewar Onyeuko, a Jihar Kaduna da Neja, rundunar Operation Thunder Strike ta samu nasarar sheke ‘yan ta’adda 34 tare da amshe bindigogin toka guda 14 da babura 17 daga hannunsu tsakanin dan datsin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164