Sojojin Najeriya Sun Sheƙe 'Yan Ta'adda 80 a Arewa Maso Tsakiya: DHQ

Sojojin Najeriya Sun Sheƙe 'Yan Ta'adda 80 a Arewa Maso Tsakiya: DHQ

  • Hedkwatar rundunar tsaro ta ce sojoji sun sheke fiye da ‘yan ta’adda 80 cikin makwanni biyu a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya
  • Darektan watsa labaran soji, manjo janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja
  • Ya bayyana yadda dakarun sojin suka samu nasarar kwace miyagun makamai tare da halaka su tsakanin ranar 24 ga watan Maris da 7 ga watan Afirilun 2022

Abuja - Hedkwatar rundunar tsaro da ke Abuja ta bayyana yadda dakarun soji suka samu nasarar halaka ‘yan ta’addan akalla 80 cikin makwanni biyu a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, Daily Trust ta ruwaito.

Sojojin Najeriya Sun Sheke 'Yan Ta'adda 80 a Arewa Maso Tsakiya: DHQ
Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan Ta'adda 80 a Arewa Maso Tsakiya, In Ji Hedkwatar Tsaro. Hoto: The Punch.
Asali: Depositphotos

Darektan labaran sojin, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai dangane da ayyukan da sojojin suka aiwatar tsakanin ranar 25 ga watan Maris zuwa ranar 7 ga watan Afirilu a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun farmaki asibiti da kwalejin mata a jihar Borno

A cewar Onyeuko, a Jihar Kaduna da Neja, rundunar Operation Thunder Strike ta samu nasarar sheke ‘yan ta’adda 34 tare da amshe bindigogin toka guda 14 da babura 17 daga hannunsu tsakanin dan datsin.

Sojin sama sun kashe wasu ‘yan ta’adda da ke tafe kan baburansu a Kauyen Mangoro

Ya ce rundunar sojon sama ma samu nata nasarorin yayin da a ranar 30 ga watan Maris ta aiwatar da harbe-harbe ta sama akan ‘yan ta’addan da ke kan baburansu a kan titin Akilibu-Sarkin Pawa da ke kauyen Mangoro, tsakanin Jihar Kaduna da Neja.

Ya ce sojojin saman sun halaka ‘yan ta’adda da dama kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya kara da bayyana yadda sojin sama duka hango ‘yan ta’adda wuraren Kusasu a ranar 31 ga watan Maris, inda suka halaka akalla guda 33.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga tasku: ‘Yan sanda suka fara sintiri ta sama a hanyar Abuja-Kaduna

Karkashin rundunar Operation Safe Haven, kakakin rundunar sojin ya ce suna ci gaba da samun nasarorin sakamakon ayyukan da suke aiwatarwa.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel