An Shawarci Al'umma Su Ƙauracewa Naman Shanu Na Sati Ɗaya Bayan Shanu 20 Sun Yi Mutuwar Ban Mamaki a Kogi

An Shawarci Al'umma Su Ƙauracewa Naman Shanu Na Sati Ɗaya Bayan Shanu 20 Sun Yi Mutuwar Ban Mamaki a Kogi

  • An shawarci mazauna Kogi da su kiyaye cin naman shanu na tsawon mako daya bayan mutuwar ban al’ajabin da shanu 20 suka yi a Lokoja
  • Darektan harkokin dabbobi na ma’aikatar noma da kiwon jihar Kogi, Salau Tarawa ya bayar da shawarar yayin tattaunawa da manema labarai ranar Alhamis
  • A cewarsa, akwai yiwuwar shanun sun ci wani abu mai guba ne yayin da suka fita kiwo kuma yanzu haka naman wasu daga cikin shanun yana kasuwa

Kogi - An bai wa mazauna Kogi shawarar dakatawa daga cin naman shanu na tsawon mako guda bayan wata mutuwar ban al’ajabin da shanu 20 suka yi a Lokoja, babban birnin jihar, The Cable ta ruwaito.

A ranar Alhamis, Salau Tarawa, darektan harkokin dabbobi na ma’aikatar noma da kiwon jihar ya bayar da wannan shawarar yayin tattaunawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje

An Shawarci Al'umma Su Ƙauracewa Naman Shanu Na Sati Ɗaya Bayan Shanu 20 Sun Yi Mutuwar Ban Mamaki a Kogi
An shawarci mazauna Kogi da su kiyayi cin naman shanu na mako daya bayan shanu 20 sun mutu. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ta yiwu naman wasu daga cikin shanun yanzu haka yana kasuwannin Lokoja kuma akwai yiwuwar wani abu mai guba dabbobin suka ci suka mutu.

Ya lissafo sunayen kasuwannin

Ya ce kamar yadda Premium Times ta nuna, an kai naman zuwa kasuwannin Osara da ke karamar hukumar Adavi, Ajaokuta, Obajana, Kotonkarfe da Kakanda duk don a siyar.

Ya kara da bayyana cewa yanzu haka ma’aikatarsu da jami’an tsaro sun hada kai wurin yin bincike akan lamarin.

Yayin bayani akan lamarin, Bayode Emmanuel, shugaban yankin harkokin noma da kiwo na hukumar tsaro ta fararen kaya, NSCDC, ya ce an ga wasu shanun a Lokoja.

Daga gama cin abincinsu yayin kiwo suka fara fadi suna mutuwa

A cewarsa:

“An ga dabbobin a bayan ofishin gwamnatin jihar, inda suka je kiwo. Nan da nan suka fara nuna wasu irin alamu daga nan suka dinga faduwa suna mutuwa.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

“Bayan tambayar mai kiwon, ya ce yana kokarin koro shanun bayan kammala kiwo kawai ya ga suna fadi suna mutuwa.”

Emmanuel ya tabbatar wa mazauna yankin cewa NSCDC za ta yi iyakar kokarinta wurin gano inda shanun suka yi kiwo sannan za ta dakatar da cin naman dabbobin da lamarin ya shafa.

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

A bangare guda, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel