Dan majalisar dokokin jihar Anambra ya sauya sheƙa daga APC zuwa APGA bayan wata 7

Dan majalisar dokokin jihar Anambra ya sauya sheƙa daga APC zuwa APGA bayan wata 7

  • Ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Cater Dike-Umeh, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa APGA
  • Ya ce ya sake dawowa APGA da take gida a gare shi saboda ba shi da dalili da zai kafa na barinta watanni Bakwai da suka shuɗe
  • Ya sanar da matakin da ya ɗauka ne a zaman majalisar dokokin Anambra na ranar Alhamis, ya samu tarba mai kyau

Anambra - Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Aguata a jihar Anambra, Cater Dike-Umeh, ya sake komawa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA).

Dike-Umeh ya sanar da komawarsa APGA ne a zaman majalisar dokokin jihar Anambra ranar Alhamis, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Dan majalisar dokoki a Anambra, Cater Dike-Umeh.
Dan majalisar dokokin jihar Anambra ya sauya sheƙa daga APC zuwa APGA bayan wata 7 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ɗan majalisar, wanda mutanen mazaɓarsa suka zaɓa karkashin inuwar APGA, ya koma jam'iyyar APC a watan Satumba, 2021.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufa'i ya yi gaskiya, hanya ɗaya ce ta kawo karshen yan ta'adda, Tinubu ya magantu

Meyasa ya koma tsohuwar jam'iyyarsa?

Da yake bayyaana komawa APGA, Honorabul Dike-Umeh, ya ce ba shi da wasu dalilai na gaskiya da suka sa ya bar jam'iyyar tun da farko.

A jawabinsa ya ce:

"Ina farin cikin sanar da wannan majalisar cewa na yi amai na lashe kuma na sake dawo wa jam'iyyar APGA wacce take tamkar gida a wuri na."
"Cikin ƙanƙan da kai, ina mai miƙa sakon neman afuwa ga shugabannin jam'iyya tun daga matakin ƙasa, jiha da gunduma saboda bani da wata gaskiya na barin jam'iyya tun a farko."
"Ina mai sanar da wannan gida cewa na samu kyakkyawan tarba a jam'iyya ta da take gida a wuri na APGA."

Okechukwu Okoye, mamba mai wakiltar mazaɓar Aguata II, shi ne ya tarbi abokin aikinsa da kyakkyawan maraba zuwa APGA.

Kara karanta wannan

Shugaban matasan APC ya yi murabus daga muƙaminsa, ya bi sahun su Kwankwaso zuwa NNPP

Bayan kammala waɗan nan abubuwa ne da sauran su, Majalisar dokokin ta ɗage zamanta zuwa ranar 12 ga watan Afrilu, 2022.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun kashe wani fitaccen Attajiri a Katsina da Azumi

Wasu yan bindiga sun yi ajalin wani fitaccen ɗan kasuwa maiɓtausayin Talakawa a yankin Kankara ta jihar Katsina.

Wani mazaunin yankin da abun ya faru ya ce maharan sun shiga kai tsaye gidan Alhaji Auta, suka fito da shi waje kuma suka kashe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel