Yanzu Haka: 'Yan Ta'adda Suna Can Sun Kai Hari A Wani Gari A Jihar Neja, Suna Cin Karensu Babu Babbaka

Yanzu Haka: 'Yan Ta'adda Suna Can Sun Kai Hari A Wani Gari A Jihar Neja, Suna Cin Karensu Babu Babbaka

  • Yan fashin daji suna can sun kai hari a garin Daza da ke karkashin karamar hukumar Munya a Jihar Niger
  • Wani mazaunin garin, Nurudeen Isyaku Daza ya ce tun karfe 5 na yamma suka isa garin suna cin karensu babu babbaka
  • Majiyoyi daga garin sun tabbatar da harin duk da cewa ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan Neja ba don bai amsa sako ba har zuwa lokacin hada rahoton

Jihar Niger - Yan fashin daji suna can sun kai farmaki a garin Daza da ke karamar hukumar Munya a Jihar Niger.

Shaidu, wanda suka tabbatarwa Daily Trust da harin sun ce mutane da dama sun tsere daga gidajensu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin bude baki, sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da wasu

Yanzu Haka: 'Yan Ta'adda Suna Can Sun Kai Hari A Wani Gari A Jihar Neja
'Yan Bindiga Suna Can Sun Kai Hari A Wani Gari A Jihar Neja. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa yan bindigan sun kutsa garin ne misalin karfe 5 na yamma kuma suka sace mutane masu yawa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun, da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Masarautu Da Tsaron Cikin Gida, ba su amsa sakonnin da aka tura musu ba.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da harin, ya ce su sace mutane da dama

Amma, wani mazaunin garin mai suna Nurudeen Isyaku Daza, ya ce yan bindigan suna can suna cin karensu babu babbaka.

"A yanzu da muke magana, ba za mu iya tantance ainihin adadin mutanen da aka sace ba domin har yanzu yan bindigan suna gidan garin. Mutane da dama sun gudu sun bar gidajensu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

An sha kai wa garuruwa da dama da ke karamar hukumar Manya hari cikin makonni biyu da suka gabata.

'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama

A wani labarin, A ranar Talata ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.

An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel