2023: Muna Buƙatar Jarumai Iri Na Domin Ceto Najeriya Daga Mutuwa, In Ji Wike

2023: Muna Buƙatar Jarumai Iri Na Domin Ceto Najeriya Daga Mutuwa, In Ji Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya ce yana da karfi da kuma jajircewar da ake bukata a wurin zaben shugaban kasar Najeriya na shekarar 2023
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin tattaunawa da jiga-jigan jam’iyyar PDP na Jihar Gombe yayin da ya ke kamfen saboda yadda zaben fidda gwani ya karato
  • A cewarsa, kada ‘yan jam’iyyar na jihar su yi asarar kuru’unsu wajen tsayar da wanda suka san ba zai lashe zaben 2023 na kasa gaba daya ba

Jihar Gombe - Nyesom Wike, gwamnan Jihar Ribas ya ce yana da iko da karfin da ake bukata a zaben shugaban kasar da zai ceto Najeriya a shekarar 2023, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da jagororin jam’iyyar PDP na Jihar Gombe yayin yawon kamfen din zaben fidda gwanin jam’iyyar da ke karatowa inda ya ce Najeriya tana bukatar jajirtattu irinsa don su ceto ta daga mutuwa.

2023: Muna Buƙatar Jarumai Iri Na Domin Ceto Najeriya Daga Mutuwa, in Ji Wike
2023: Muna bukatar jajirtattun mutane iri na don ceto Najeriya daga mutuwa gaba daya, Wike. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Gwamnan ya bukaci jiga-jigan jam’iyyar na jihar da su kiyaye asarar kuru’unsu wajen zaben fidda gwani ga wanda suka san ba zai iya lashe zaben kasa na 2023 ba.

Wike ya ce rashin tsaro bai san addini ko yare ba

The Cable ta ruwaito inda ya ce:

“Idan kuna son PDP ta lashe zabe a 2023, ga ni na gabatar da kaina. Ku tsayar da ni kuma ku ba ni damar mulki. Muna magana ne akan wanda zai iya kwace mulki daga hannun APC, kuma ni ne.

Kara karanta wannan

Ku shigo NNPP: Kwankwaso ya yi kira ga matasa su shigo NNPP domin ceto Najeriya

“Muna bukatar taimako a kasar nan, kada mu yi kamar ba haka bane. Rashin tsaro bai san addini ba. Rashin tsaro bai san yanki ko yare ba. Talauci bai sai yare ba, bai kuma addini ba.
“Mutanen nan da ke zuwa suna kashe mu ba sa duba kirista. Ba sa duba musulmai. Ko sun san Hausa-Fulani? Sun san kabilar Ibo? Kawai mutuwa muke ta yi.”

Ya musanta batun gwamnatin tarayya na jajircewa a harkar noma

Kamar yadda ya ce, a cire son rai a tsaya akan gaskiya. Idan aka ba shi dama, zai yi abinda ya yi a Jihar Ribas a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya.

Wike ya zargi shugabancin APC da yin karairayi dangane da ci gaban noman kasar nan. Ya ce gwamnati ba ta cika alkawuran da ta dauka.

Ya musanta batun da gwamnati ta yi na bayar da Naira biliyan 300 ga noma inda ya ce ba matsalarta bane wannan. Ya ce kullum cikin siyan hatsi ake a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kada Wanda Ya Zarce Shekaru 70 Da Haihuwa Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, Ortom

'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

A bangare guda, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164