'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama
- Wasu ‘yan bindiga sun kai wa masu ibada farmaki har masallaci a ranar Talata suna tsaka da buda-baki bayan sun kai azumi
- ‘Yan ta’addan wadanda sun kai mutane 50 sun halaka mutane 3 sannan sun yi garkuwa da wasu jama’an da dama
- Lamarin ya auku ne a kauyen Baba Juli da ke karkashin karamar hukumar Bali a Jihar Taraba kamar yadda mazauna kauyen suka shaida
Taraba - A ranar Talata ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.
An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.
‘Yan ta’addan sun kai farmaki kauyen a watan da ya gabata amma sun tsere bayan ‘yan kauyen sun dinga musayar wuta da su.
Sun mamaye su ne in ji wani mazaunin kauyen
Wani mazaunin kauyen, wadanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce:
“Sun mamaye mu ne lokacin da suka kai mana farmakin. Muna tsaka da buda-baki a cikin masallaci sai dai muka ji harbe-harbe kuma babu yadda muka iya yi da su.”
Ya ce mutane uku sun rasa rayukansu a masallacin sakamakon harin kuma an kwashe ‘yan kauyen da yawa zuwa inda ba a sani ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce ya na jiran samun bayanai daga ofishin ‘yan sandan da ke Bali.
'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto
A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.
Asali: Legit.ng