Abin da ka raina: Yadda matashi ya dauki hoton makadi, ya sayar N1.2m a duniyar Crypto

Abin da ka raina: Yadda matashi ya dauki hoton makadi, ya sayar N1.2m a duniyar Crypto

  • Wani hazikin madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya mayar da hotunan da ya dauka na wani dattijo makadi ya zama masa arziki cikin kankanin lokaci
  • Kwanaki bayan da ya dauki hoton, Adisa ya daura shi a kafar cinikayyar NFT ta OpenSea inda ya sayar da su a kan 0.6Eth/$2,098.32 (daidai da N2,042,440.72)
  • 'Yan Najeriya da dama da suka mayar da martani ga wannan aiki sun so sanin yadda za su yi su iya kasuwancin NFT da kuma samun kudi cikin gaggawa

Wani matashi madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya nuna daya daga cikin damammaki masu yawa na duniyar kudaden intanet wato blockchain da cryptocurrency ta kunsa.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, Adisa ya ce ya dauki hotunan wani tsohon makadi wanda ya saba gani a hanyarsa ta zuwa hidimar ci gaban al’umma ta CDS ta NYSC.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata a sani a tarihin Sanata Dansadau wanda ya tsige Imam Nuru Khalid

Tsohon makadi ya shiga duniyar Crypto
Abin da ka raina: Yadda matashi ya dauki hoton makadi, ya sayar N1m a duniyar Crypto | Hoto: @adisaolashile
Asali: Twitter

Yadda ya mayar da hoton makadi zuwa kudi

A ranar Asabar, 2 ga Afrilu, madaukin hotunan ya hau Twitter inda ya bayyana cewa ya sauya hotunan tsohon makadin zuwa Non-Fungible Token (NFT) a kasuwar OpenSea kuma ya sayar da su akan 0.3 Ethereum (Eth) kowanne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton farashin Eth/USDT ya kai $3497.33 (daidai da N2,042,440.72) kuma ana sayar da 0.3 na Eth akan kudi $1049.19 akan manhajar Binance. Tare da sayar da hotuna biyu kan 0.3 Eth kowanne, zai zama $2,098.32 (N1,225,418.88) a farashi.

Zan bashi 50%

Adisa ya ce 50% na kudin da ya samu na hoton zai kai wa makadin. Ku sani cewa farashin crypto ba shi da tabbas kuma farashin ka iya canzawa a kowane lokaci.

Martanin 'yan Twitter

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a karkashin rubutunsa.

Kara karanta wannan

Adadin talakawan da ke rayuwa Najeriya ya na tashi, zai kai miliyan 95 a shekarar nan

@DcOmomeji ya ce:

"Na rantse da kwamfutar tafi-da-gidanka na hana ni samun damammakin da ya kamata na koya. Ya Allah ka aiko da mai taimako ya albarkace ni da tsohuwa ko sabuwa pls."

@Phunshood ya amsa:

"Ba lallai bane ka bukaci kwamfutar tafi-da-gidanka don farawa, kana amfani da iphone, ka riga ka sami abin da kake bukata."

@Tee_Classiquem1 ya ce:

"Kai, wannan yana da kyau...don Allah ta yaya zan iya sayar da kaya akan NFT nima?"

@Dokwuagwu said:

"Dakata.. Aboki don Allah da iPhone ka yi amfani wajen daukar wannan hoton.. Domin gani nake kamar ban taba amfani da wayata wajen yin wani abu ba."

@HeykinsHawkins ya ce:

"Da alama dai ya kamata na koyi wannan NFT din."

Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT

A wani labarin, Daniel Maegaard a da yana samun Naira 6,500 kacal a kowane awa idan ya yi aiki a wani gidan mai a karshen mako yayin da yake karatun ilimin halayyar dan adam a wata Jami'ar.

Kara karanta wannan

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

Maegaard ya kasance yana tara kwabban crypto yayin da yake hada aikinsa da karatu amma gogewa a fannin fasaha da sa'ar rayuwa sun sa ya zama hamshakin attajirin dare daya.

Ya yi tuntube da wani tsagin duniyar crypto da ake kira Non Fungible Tokens (NFTs) shekaru kafin su zama abin da suke yanzu. Wannan ya ba shi damar zama miloniya a cikin shekaru goma da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.