Innalillahi: 'Yan bindiga sun bindige dan kwamishinan tsaron Zamfara lokacin buda baki
- Mummunan labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun hallaka dan kwamishinan tsaro a jihar Zamfara
- Wannan na zuwa ne yayin da hare-haren 'yan bindiga ke kara kamari a yankunan Arewa maso Yammacin kasar nan
- An ruwaito yadda 'yan bindigan suka shiga garin Tsafe tare da bindige dan kwamishinan da wasu mutane
Zamfara - Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an harbe dan DIG Ibrahim Mamman Tsafe (rtd), kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara mai ci.
Rahoto ya bayyana cewa, an kashe dan kwamishina Tsafe ne tare da wasu mutane uku a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari garin Tsafe, hedikwatar karamar hukumar Tsafe ta jihar a daren jiya Lahadi.
A baya-bayan nan dai, garin Tsafe da wasu yankuna da dama a cikin karamar hukumar sun sha fama da munanan hare-hare da garkuwa daga trsagerun 'yan bindiga.
Watanni biyu da suka gabata an kashe wani mazaunin garin da jami’in kwastam a wasu hare-hare da aka kai a garin.
A watan Fabrairun da ya gabata ne ‘yan bindigar suka harbe wani limami a lokacin da yake kiran sallar Asuba a garin Magazu da ke da tazarar kilomita 5 Kudu da garin na Tsafe.
Su waye 'yan bindigan da suka kashe dan kwamishina?
‘Yan ta’addan da ake kyautata zaton suna tserewa ne daga ragargazar soji a wasu sassan jihohin Arewa maso Yamma suka fara kaura zuwa yankunan karamar hukumar Tsafe domin fakewa.
A wasu mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, ‘yan ta’addan sanye da kayan sojoji sun kai farmaki unguwar Shiyar Namada da ke kusa da gidan kwamishinan inda suka bude wuta kan mutane.
A cewar wani mazaunin yankin mai suna Umar:
“Wasu mazauna garin da suka gan su tun da farko sun dauka jami’an tsaro ne da ke sintiri na yau da kullum. Wasu daga cikinsu ba su damu su ankarar da jama'a ba.
“Dan kwamishinan, tare da wasu mutane suna zaune a gaban gidan DIG Ibrahim Mamman Tsafe a lokacin buda baki, kwatsam sai ga ‘yan bindigar sun fito suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
“A yayin harin, galibin mutanen da ke sallar Tarawihi a masallatai da dama da ke kewayen yankin kuma mazauna yankin sun gudu domin tsira. Daga baya ‘yan bindigar sun guda zuwa cikin dajin. Yayin da nake magana da ku, ina gidan Waziri ne inda ake shirye-shiryen jana’izar su.”
Wasu mazauna garin sun shaida cewa, harin na iya zama ramuwar gayya, saboda kisan da aka yiwa wani da ake zargin dan bindiga ne da aka gani a kofar garin a ranar Juma’ar da ta gabata.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Ayuba Elkanah, ya ziyarci garin domin jajantawa DIG mai ritaya da kuma tantance barnar nan take, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC
A wani labarin, har yanzu ba a ji duriyar mutum dari da arba'in da shida cikin fasinjoji 362 da ke cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, kwanaki shida bayan harin da 'yan ta'adda suka kai kan jirgin.
Manajan daraktan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka samo a ranar Litinin 4 ga watan Afirilu.
Rahoton Punch ya bayyana cewa, adadin fasinjojin da suka tsira ya karu zuwa 186 tun bayan harin na kwanakin nan.
Asali: Legit.ng